✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya roki Gwamnatin Tarayya ta sake bude filin jirgin saman Kano

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta sake bude reshen filin jirgin saman kasa-da-kasa na Malam Aminu Kano bayan shafe…

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta sake bude reshen filin jirgin saman kasa-da-kasa na Malam Aminu Kano bayan shafe tsawon watanni a rufe.

A cikin sanarwar da Babban Sakataren Labarai na Fadar Gwamnati ya fitar a ranar Laraba, ya ce Gwamnan ya gabatar da wannan bukata ne a yayin da ya ziyarci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata.

Gwamnan ya yi bayanin cewa ci gaba da hana ayyukan tashi da saukar jiragen saman kasa-da-kasa yana matukar shafar jihar Kano a matsayinta na cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya.

“A madadi gwamnati da jama’ar jihar Kano, ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta bude reshen filin jiragen saman kasa-da-kasa na Malam Aminu Kano da aka kammala aikin fadadawa,” a cewar Ganduje.

A nasa jawaban, Hadi Sirika ya bai wa gwamnan tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a dawo da ayyukan zirga-zirgar fasinjojin kasa-da-kasa a filin jirgin saman da aka kammala aikinsa.

“Nan ba da dadewa ba za a fara aiki da reshen zirga-zirgar kasa-da-kasa na filin jirgin saman Malam Aminu Kano.”

“Mai girma Gwamna nima daga Kano nake kuma Kano jihar ta ce, saboda haka ina kira ga mutanen Kano da su bai wa Gwamnatin Tarayya hadin kai a kan wannan batu,” a cewar Ministan.

Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan ayyukan ci gaba da Gwamnatin Tarayya ta aiwatar a Kano, yana mai cewa, “irin wadannan ayyuka da makamantansu suna kara bunkasa tattalin arzikin jiharmu.”

Ana iya tuna cewa, a watan Satumbar bata ne Gwamnatin Tarayya ta sake bude ayyukan jigilar fasinjojin kasa-da-kasa bayan rufe sun a tsawon watanni shida domin dakile yaduwar annobar Coronavirus da ta gurgunta tattalin arzikin kasashen duniya.