✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya sake korar tsohon Kwamishinan da ya yi ’murna’ da mutuwar Abba Kyari

Wannan da shi ne karo na biyu da Ganduje yake korarsa a shekara biyu.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Injiniya Mu’az Magaji (Dan Sarauniya) daga mukamin shugabancin kwamitin Jihar Kano da ke kula aikin shimfida bututan iskar gas na AKK.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Gwamnan yake korarsa daga aiki cikin shekara biyu.

Ko a shekarar 2020 dai Ganduje ya sauke shi daga mukamin Kwamishinan Ayyuka na Jihar bayan da ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook da ke alamta cewa yana murna da mutuwar Abba Kyari, tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya mutu sanadiyyar COVID-19.

A cewar wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya fitar a daren Litinin, an dakatar da shi a wannan karon ne saboda rashin tabuka wani abin ku-zo-ku-gani da kuma wuce gona da iri.

An dai nada shi ne ya shugabanci kwamitin a watan Afrilun 2020, don ya tabbatar da nasarar aikin na shimfida bututan daga Ajaokuta zuwa Kano wanda Gwamnatin Tarayya ke yi.

Sai dai sanarwar ta zarge shi da cewa bai tsinana komai ba  tsawon lokacin da aka nada shi.

Tuni dai aka umarce shi da ya mika ragamar kwamitin ga Mataimakinsa, Aminu Babba Dan-Agundi, Sarkin Dawaki Babba.