Ganduje ya sauya wa jami’ar Kano suna zuwa Aliko Dangote | Aminiya

Ganduje ya sauya wa jami’ar Kano suna zuwa Aliko Dangote

Alhaji Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote
    Sani Ibrahim Paki

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da sauya wa Jami’ar Kimiyya da Fasaha (KUST) da ke Wudil a Jihar, suna zuwa na hamshakin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

Daukar matakin, a cewar Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba, ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwa Jihar ne yayin zamanta na mako-mako.

Ya ce hakan kuma na cikin shawarar da Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta bayar.

Muhammad Garba ya tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar ta ce yanzu za a rika kiran sunan makarantar da sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUST) da ke Wudil.

Kwamishinan ya ce tuni aka aike da bukatar canza sunan a hukumance ga Majalisar Dokokin Jihar ta Kano domin ta amince da shi ya zama doka.

Alhaji Aliko Dangote, wanda shi ne attajiri mafi kudi a nahiyar Afirka dai dan asalin Jihar ta Kano ne.

Jami’ar kuma a daya bangaren na daya daga cikin jami’o’i guda biyu mallakin gwamnatin Jihar.

Ko a shekarar 2018 sai da Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya canza wa Jami’ar Northwest, ita ma mallakin Jihar suna zuwa Yusuf Maitama Sule.