✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya yi gargadi kan yakin zabe a wuraren ibada

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi ’yan siyasaa da su guji amfani da wuraren ibada wajen gudanar yakin neman zabe.

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gargadi ’yan siyasaa da su guji amfani da wuraren ibada wajen gudanar yakin neman zabe.

Gwamnan ya yi gargadin ne a jawabinsa a wani taro na kasa na mallaman addinai daban-daban karo na hadu wanda aka yi a jihar Kano a ranar Alhamis.

Gwamnan ya kuma yi kira ga masu yakin nemen zaben da su kiyaye da ka’idar Hukumar INEC da ta haramta yin yakin nenan zaben a wuraren ibada.

Sannan ya yi tir da yadda wasu ’yan siyasa ke amfani da addini wajen raba kawunan jama’a, musamman a lokacin zabe domin biyan bukatar kansu.

Gwamna Ganduje ya yi kira ga shugabannin addinan a Najeriya da su hada  kansu ta hanyar fahimtar juna da kuma tattaunawa don wanzar da zaman lafiya da hadin kai domin cigaban kasa.

Taron wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyi, Dakta Muhammad Bin Othman ne yake shugabanta yayin da Bishof na yankin Arewa Peter Ogunbiyi ke matsayin shugaba na biyu.