✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya yi wa kungiyoyin kwallon kafan Kano yayyafin N96m

Ganduje ya ce wasanni na taimakawa wajen nisantar da su daga munanan dabi'u,

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa kananan kungiyoyin kwallon kafa 47 na Jihar kyautar Naira 96m domin tallafa masu wajen shirye-shiryen wasannin wannan shekara.

Ganduje, wanda Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta a wajen wani gagarumin bikin da aka gudanar a dakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnatin Jihar, ya dai bayar da tallafin Naira miliyan uku ne ga kowacce kungiya a matsayin ajin farko.

Kazalika, Gwamnan ya kuma ba kungiyoyi 29 miliyan biyu, sai kuma miliyan daya ga kungiyoyi takwas na aji na uku.

Da yake jawabi yayin bayar da kudaden, Gwamnan ya ce, “Wannan alkawari ne da gwamnatin Jihar ta yi kuma ta cika.

“Muna jinjina ga masu kulob din kan yadda suke tafiyar da kungiyoyin da kuma jawo hankalin matasa kan abin da ya shafi wasanni domin hakan zai taimaka wajen nisantar da su daga munanan dabi’u,” inji Gwamnan.

Ganduje ya kuma yi godiya da yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Jihar take kaddamar da gasar wasanni ga matasa a jihar.

Da yake jawabi Kwamishinan Matasa da Cigaban Wasanni, Kabiru Ado Lakwaya ya bayyana tallafin kudin a matsayin wani shiri na ci gaban dan Adam da gwamnatin Ganduje take yi domin bunkasa harkokin wasanni.