✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa

Ganduje ya ce za a yi rashin sa matuka saboda abubuwa da dama.

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya taya tsohon Gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso alhinin rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

Marigayin, wanda kafin rasuwarsa shi ne Hakimin Madobi kuma Makama, daya daga cikin masu zabar sarki a Masarautar Karaye ta jihar ya rasu da sanyin safiyar Juma’a yana da shekara 93 a duniya.

Ganduje, a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana kaduwarsa da rasuwar.

Gwamnan ya kara da cewa za a yi rashin Alhaji Musa Kwankwaso saboda dimbin gudunmawar da ya ba al’umma da kuma gogewa da hangen nesarsa a matsayinsa na mai rike da sarauta.

“A madadin ni kaina, iyalaina, gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano, ina mika sakon ta’aziyya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Masarautar Karaye da ma Jihar Kano saboda rashin Makama, wanda ya shafe kimanin shekara 20 yana rike da sarautar Hakimin Madobi.

“Marigayin ya nuna sadaukarwa da jajircewa, kuma Musulmi ne mai riko da addini matuka.

“Ya bar mana nagartattun halaye abubuwan koyi kamar yafiya, adalci, gaskiya da kuma hidimta wa jama’arsa.

“Hakika mun yi babban rashi musamman a irin wannan lokaci da ake bukatar gogewa irin tasa,” inji Ganduje.

Gwamna Ganduje ya kuma ce Alhaji Musa Kwankwaso ya bar kyawawan manufofi da za a jima ana tunawa da shi, kuma ya hidimta wa al’umma, ba iya na masarautarsa kadai ba, har ma da Kano, Najeriya da duniya baki daya.

Daga nan sai gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya jikan sa ya kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashin.

A watan Nuwamban da ya gabata ne dai Sarkin Karaye, daya daga cikin sabbin Masarautu hudun da Gwamna Ganduje ya daga likkafarsu a jihar ya daga darajar mahaifin Kwankwason daga Majidadi zuwa Makaman Karaye kuma daya daga cikin masu zabar sarki a masarautar.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 19 da kuma jikoki da dama.