✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya yi rusau a kusa da Gidan Nasiru Kabara

Ginin a ya haifar da zargi tsakanin Gwamantin Ganduje da Masarautar Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya rusa wani ginin kasuwanci a kusa da gidan fitaccen jagoran Darikar Kadiriyya, Marigayi Sheikh Nasiru Kabara.

Ginin, wanda ke wani fili mallakin Masarautar Kano, Gwamna Ganduje ya sa a rushe shi ne, saboda an yi shi ne ba tare da sahalewar gwamnatin jihar ba.

Manajan Daraktan Hukumar Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA) kuma Shugaban Kwamitin Rusa Gine-ginen Da Aka Yi Ba Bisa Ka’ida Ba, Baffa Babba Dan’agundi, ya ce daga Gwamnatin Jihar Kano har Masarautar Kano babu wanda ya ba da izinin yin ginin.

Dan’agundi, ya ce baya ga rade-radin da ake yadawa, “Ya kamata mutane su sani cewa yin ginin ya haifar da zargi tsakanin gwamantin jihar da masarauta, duk kuwa da cewa a cikinsu babu wanda ke goyon bayan yin ginin.

“Bayan gudanar da bincike, an gano cewa wasu masu son zuciya, wadanda kansu kawai suka sani ne suke da ginin.

“A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Ganduje ya ba da umarnin rushe ginin, tare da katange wurin domin mayar da shi dandalin wasan yara.

“Ragowar filin kuma za a ci gaba da amfani da shi wajen gudanar da zikirin Darikar Kadariyya kuma shi ma za a katange shi.”

Ya ce gwamnan ya sa girke a jami’an tsaro a koyaushe a wurin domin bayar da kariya ga yara masu wasa da iyayensu daga ayyukan bata-gari.

Dan’agundi ya gargadi mutane da su guji yin gine-gine ba bisa ka’ida ba, saboda Gwamnatin Jihar Kano, “Ta dauke matakin gurfanar da duk wanda ya aikata hakan a gaban kuliya.