✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gani ya kori ji: Dusar kankar farko da mahaukaciyar guguwa a Amurka

Muhimman abubuwa da masu daukar hankali da dama sun auku a makon nan mai karewa.

Muhimman abubuwa da masu daukar hankali da dama sun auku a makon nan mai karewa.

Ga kayatattun hotunan wasu daga ciki:

Wani mutum na wucewa a gaban wani abin adon bikin Kirsimeti da aka girke a gaban gidan wasan kwaikwayo na Bolshoi a tsakiyar birnin  Moscow na kasar Rasha, ranar 14 ga Disamba, 2021. (Hoto: Yuri KADOBNOV/AFP).
Shugaban Amurka Joe Biden yana magana da wata ‘yar kasar yayin da ya je duba irin barnar da mahauciyar guguwa ta yi a Dawson Springs, Kentucky, a ranar 15 ga Disamba, 2021. (Hoto: Brendan SMIALOWSKI/AFP)
Wani jirgin ruwa na kamfanin RNLI (Royal National Lifeboat Institution) ya taimaka wa bakin haure a bakin tekun Dungeness da ke Kudu maso Gabashin gabar tekun Ingila a ranar 16 ga Disamba, 2021. (Hoto: Ben STANSALL / AFP).
Wani sanye da kayan ‘Santa Claus’ na bikin Kirsimeti yana hawan igiyar ruwa a cikin ruwa mai tsananin sanyi a  tafkin Alaia Bay wanda ke kewaye da Swiss Alps a Sion ranar 15 ga Disamba, 2021. (Hoto: Fabrice COFFRINI / AFP).
Yadda wani sojan kasar Yukren ke kan gaba yayin fita daga wani wurin buya yayin da suke gwabza yaki da ‘yan a-waren da ke samun goyon bayan Rasha a kusa da kauyen Pesky na yankin Donetsk, a ranar 14 ga Disamba, 2021. (Hoto: Anatolii STEPANOV/AFP).
Kitty Williams ke nan, wacce ta tsira daga mahaukaciyar guguwar Bowling Green a Amurka tana rike da wani allo mai dauke da rubutun godiya ga  abokai da danginta da suka taimaka wajen tattara kayanta da suka rage bayan guguwar a Kentucky a ranar 13 ga Disamba, 2021 (Hoto: Gunnar Word / AFP).
Yadda wani mai goyon bayan jam’iyyar adawa ta NUP a kasar Yuganda ya tare hanya yayin da ‘yan sanda suka tarwatsa magoya bayan jam’iyyar gabanin yakin neman zabe na karshe na jam’iyyar, a Kayunga, ranar 14 ga Disamba, 2021. (Hoto: Badru KATUMBA / AFP)
Mutane ke kwasar guntayen dalmomi a wurin da wata tankar gas ta fashe a garin Cap-Haitie na kasar Haiti, a ranar 14 ga  Disamba  2021.   Akalla mutum 62 ne suka mutu lokacin da motar  ta fashe da safiyar ranar. (Hoto: Richard Pierrin / AFP).
Wasu matasa cikin jin dadin yadda dusar kankara ta farko ke zuba a birnin Kabul na kasar Afghanistan, ranar 15 ga Disamba, 2021. (Hoto : Mohd RASFAN / AFP).
Mutane a tsaye yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye garin Guiuan da ke gabar teku, a lardin Samar Gabashin kasar Filifins, aranar 16 ga Disamba, 2021, bayan da mahaukaciyar guguwar ta tashi. (Hoto: ALREN BERONIO/AFP)
Mutane sun rusuna wa babban hoton Kim Il Sung da Kim Jong Il, tare da yin shiru na tsawon minti uku domin karrama su a wajen bikin cikar shekara 10 da rasuwar Kim Jong Il shekara goma da mutuwa a birnin Pyongyang, ranar 17 ga watan Disamba 2021. (Hoto: KIM Won Jin/AFP).