Gani ya kori ji: Hotunan muhimman abubuwa a wannan makon | Aminiya

Gani ya kori ji: Hotunan muhimman abubuwa a wannan makon

Wani dan sanda a Indiya yana sanyaya fuskarsa da ruwa saboda tsananin zafi
Wani dan sanda a Indiya yana sanyaya fuskarsa da ruwa saboda tsananin zafi
    Abdullahi Abubakar Umar

Wasu daga cikin muhimman hotunan abubuwan da suka faru a wannan makon:

Rasha ta yi ruwan bama-bamai a birnin Mariupol na kasar Ukraine a ci gaba da mamayar da ta kai kasar. (Hoto: AFP).

Wahalar man fetur ne ci gaba da gasa wa mazauna Birnin Tarayya Abuja gyada a ka.

Dalibai sun gudanar da zanga-zanga a Legas bayan Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU) ta tsawaita yajin aikinta da wata uku.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Kawu Sumaila da Abdulmumini Jibrin Kofa da Rurum a filin jirgin Mallam Aminu Kano a yau Juma’a 13 ga watan Mayun 2022. (Hoto: Hon. Saifullahi Hassan)

Uwargidan Shugaban Amurka, Jill Biden, ta kai wa takwararta ta Ukraine, Olena Zelenskyy, ziyarar ba-zata a wata makaranta da aka tsuganar da fararen hula da yaki ya raba da muhallansu. (Hoto: Facebook/AFP)