Gani Ya Kori Ji: Hotunan muhimman abubuwan da suka faru a wannan mako | Aminiya

Gani Ya Kori Ji: Hotunan muhimman abubuwan da suka faru a wannan mako

    Abdullahi Abubakar Umar

Gani Ya Kori Ji na Aminiya ya tattaro muku hotunan wasu abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku.

A yi kallo lafiya:

Shugaba Buhari ya bai wa wasu ’yan kasashen waje 286 shaidar zama ’yan Najeriya a fadarsa da ke Abuja a ranar Alhamis.

 

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Gwamnan Knao Abdullahi, Umar Ganduje, sun je ta’aziyya a gidan Sanata Kabiru Gaya bayan rasuwar dansa. (Hoto: Aminu Dahiru).

Osinbajo da Gwamna Ganduje a gidan Sanata Kabiru Gaya domin yi masa ta’aziyyar rashin dansa da ya yi. (Hoto: Aminu Dahiru).

Karin hoton Osinbajo da Ganduje a gidan Sanata Kabiru Gaya a lokacin ziyarar ta’aziyyar rasuwar dansa. (Hoto: Aminu Dahiru)

 

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye garin Auyo da ke karamar hukumar Auyon jihar Jigawa da safiyar yau Juma’a.
Hoto: Facebook/Sawaba FM 104.9 Hadejia

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye garin Auyo da ke karamar hukumar Auyon jihar Jigawa da safiyar yau Juma’a. Hoto: Facebook/Sawaba FM 104.9 Hadejia

Daliban Makarantar Al-Kur’ani ta Hamza Al-Kufi da ke Makkah, sun kai ziyara Masallachin Harami, inda aka ba su damar wanke Ka’aba domin a karrama su.
(Hoto: Haramain Sharifain).

Daliban Makarantar Kur’ani ta Hamza Al-Kufi da ke Makkah, sun kai ziyara Masallachin Harami, inda aka ba su damar wanke Ka’aba domin a karramasu. Hoto: Haramain Sharifain

Daliban Makarantar Kur’ani ta Hamza Al-Kufi da ke Makkah, sun kai ziyara Masallachin Harami, inda aka basu damar wanke Ka’aba domin a karramasu. Hoto: Haramain Sharifain

Daliban Makarantar Kur’ani ta Hamza Al-Kufi da ke Makkah, sun kai ziyara Masallachin Harami, inda aka basu damar wanke Ka’aba domin a karramasu. Hoto: Haramain Sharifain