Gani ya kori Ji: Yadda ’yan Kannywood ke atisayen wasan Sarauniyar Zazzau
An gayyaci ’yan Kannywood ta hannun kungiyar Arewa Film Makers da su gabatar da wasan kwaikwayo na dabe kan Sarauniyar Zazzau, a wani bikin baje…
DagaYakubu Liman
Thu, 30 Jun 2022 13:53:25 GMT+0100
An gayyaci ’yan Kannywood ta hannun kungiyar Arewa Film Makers da su gabatar da wasan kwaikwayo na dabe kan Sarauniyar Zazzau, a wani bikin baje kolin ala’dun gargajiya da za a yi a kasashen waje.
Wadannan hotuna, atisayen wasan da suke yi ne a karkashin kulawar Gwamnati Jihar Kwara, da tallafin Ma’aikatar Raya Al’adu ta Kasa, tare da Ma’aikatar Harkokin Waje.
Babban kwamitin shirye-shiryen gabatar da wasan bayan taronsa a Abuja. (Hoto: Kaka).Ibrahim Mandawari, shugaban kwamitin gudanar da wasan tare da Abdullahi Zakari Ligidi yana jawabi ga Shugaban Hukumar Raya Al’adun Gargajiya ta Jihar Kwara. (Hoto: Maikatanga).
Tijjani Faraga da sauran ’yan wasa na bin umarnin Daraktan wasan. (Hoto: Maikatanga).Kawu Mala na Dadinkowa da Balarabe Musa na Kwana Casa’in tare da sauran ’yan wasa. Hoto: MaikatangaTijjani Faraga tare da Jaruma Maryam Aliyu a cikin wasan. (Hoto Maikatanga)Sauran Jarumai a cikin wasan. (Hoto: Maikatanga).Salihi na Dadinkowa da sauran wasu jaruman a atisayen wasan. (Hoto: Maikatanga).Jamila Abubakar, Kawu Mala Tijjani Faraga da sauran ‘yan wasa: Hoto: Maikatanga.Jamila Abubakar wacce ta fito a matsayin Sarauniya Balarabe Tela da sauran ’yan wasa. (Hoto: Maikatanga).