✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganin ’yan bindiga ya fi sauki a kan ganin Buhari – Sheik Ahmad Gumi

A baya dai gwamnatin Buhari ta yi watsi da bukatar malamin ta yi wa ’yan bindigar afuwa a matsayin hanya daya tilo ta samun zaman…

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Kaduna, Sheik Ahmad Abubakar Gumi ya ce ganin ’yan bindiga ya fi sauki a kan ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A cewar kakakin Kungiyar Dattawan Arewa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, Sheik Gumi ya shaidawa masu ruwa da tsaki na yankin cewa duk kokarin da ya yi na ganawa da Buhari a kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya ya gaza kaiwa ga gaci.

Malamin dai ya jima a ’yan watannin da suka gabata yana fadi tashin tattaunawa da ’yan bindigar da nufin ganin an lalubo bakin zaren matsalar tsaro musamman a Arewacin Najeriya.

“A yau, Sheik Ahmad Gumi ya shaidawa taron mutanen Arewa a Kaduna yadda ya shafe watanni yana ganawa da ’yan bindiga, amma ya shafe wasu watannin da dama kuma bai sami ganin Shugaban Kasa ba kan matsalar tsaro. Ya ce ganawa da ’yan bindigar ya fi sauki nesa ba kusa ba a kan ganawa da Buhari,” inji Dakta Hakeem, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.

Sai dai jim kadan da wallafa sakon aka shiga tafka muhawara tare da kalubalantarsa a shafin, ko da yake ya yi ta kokarin kare kansa a kan hakan, inda wasu daga cikinsu ke ganin ba dole ne sai malamin ya gana da Shugaban Kasar ba.

Wasu kuma sun bukace shi da ya aike da shawarwarinsa a rubuce ga Ministan Tsaro a maimakon dagewa dole sai ya ga Shugaban Kasar ido da ido.

A baya dai gwamnatin Buhari ta yi watsi da bukatar malamin ta yi wa ’yan bindigar afuwa a matsayin hanya daya tilo ta samun zaman lafiya.