✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gara na mutu da in goyi bayan Atiku — Ortom

Ya bayyana haka ne a taron lafiyar cin abincin da ya shirya wa gwamnoni hudu na PDP a ranar Lahadi da dare.

Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ya ce babu shi, babu dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar PDP, Atiku Abubakar.

Ortom ya ce Atiku ya yi duk abin da ya ga dama, amma babu ruwansa da yakin neman zaben.

“Atiku da masu goyon bayansa su yi duk abin da suka ga dama… amma da in goyi bayan Bafullatani ya zama shugaban kasa gwanda in mutu… Ba zan taba  goyon bayan makiyin al’ummar Binuwai ba,” in ji gwmanan.

Ya bayyana haka ne a taron lafiyar cin abincin da ya shirya wa gwamnoni hudu na PDP a ranar Lahadi da dare.

Gwamnoni sun je jihar Binuwai ne gabannin taron kaddamar da yakin neman zabe na jam’iyyar da kuma ayyuka da gwamnantin Ortom ta kammala.

Gwamnonin — Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abiya, Seyi Makinde na Oyo da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Inugu — sun je Binuwai ne a karkashin kungiyar da suke kira G5.

Kungiyar da Wike ke jagoranta, na adawa ne da tsarin jami’iyyar PDP ke kai, da kuma shugabancin Iyorchia Ayu a jam’iyyar.