✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Garba Shehu ya tura sanarwar daukar aikin da aka rufe tun 2021

Ya tura sako yana kiran matasa su nemi gurabun aikin da aka riga aka rufe wata biyar da suka gabata.

’Yan Najeriya na ragargazar Hadimin Shugaban kan Yada Labarai, Garba Shehu, kan wani sako da ya wallafa yana kiran matasan kasar su nemi gurabun sanin makamar aiki a Majalisar Dinkin Duniya, alhali tun wata biyar da suka gabata aka rufe.

A yammacin rabar Alhamis ne Garba Shehu ya wallafa sakon a shafinsa na Twitter yana kiran matasan Najeriya da suka kammala jami’a su nemi gurbin sanin makamar aiki da Hukumar Raya Kasashe da Majalisar Dinkin Duniya (UNDP).

Sakon nasa, ya ce, “Matasanmu da suka kammala jami’a za su iya neman gurbi a shirin zama Mamba a Hukuamr UNDP.

“Za a dauki matasa 20,000 su yi aiki karkashin shirin sanin makamar aiki na shekara daya a kamfanoni da hukumomin ci gaban kasashe. 

“Akwai albashi mai tsoka da kuma kwarewa marar iyaka.” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan babbar dama ce, saboda haka a taimaka a taya mu yada sakon.”

Sai dai bayan bude shafin neman gurbin da ya bayar, sai ’yan Najeriya suka samu sakon cewa tun a watan Oktoban shekarar 2021 aka rufe damar, wadda aka bayar daga ranar 6 ga Satumba zuwa 20 ga watan Oktoban 2021.

Hakan ya sa aka yi ta ragargazar Garba Shehu a Twitter inda Farfesa Ashurton Grove (@M____O____B) ya yi mishi raddi da cewa, “Sai dai idan har yanzu shekarar 2021 ba ta kare ba.”

Shi ko @AkinolaKintan cewa ya yi, “Wai babban hadimin shugaban kasa ke tura wa mutane gurabun da aka riga aka rufe.

“To yanzu mene ne amfanin sakon? Shin so kake ’yan Najeriya sun nema, alhali har an riga an fara tantance wadanda suka nema?”

MJSmart (@mmohammedjamiu1) ya ce, “Yallabai ka yi kuskure. Mu ai fitowar sunayen muke jira. Tun shekarar da ta wuce aka rufe wannan damar.”

Wani mai suna, Oyedokun Oyedele (@officialTeeq), ya ce, “Kada ku wahalar da kansu, tun a watan Oktoban 2021 aka rufe.”

“Ikon Allah, wai babban jami’in gwamnati ne da tura abu ba tare da ya tantance ba,” inji king Marvel (@marvelnsa).

Mahmud Salihu Kaura (@Mahmudkaura01) ya ce, “Abin da aka rufe yin rajistansa tun a 2021, amma yanzu kake kiran matasa su nema. To me kake nufi?”

Hon. Bankyy (@Joelbanky) ta ce, “@GarShehu me ya sa za ka tura sakon adireshin gurabun da aka rufe tun wata shida da suka gabata? Ba ka kyauta ba.”

Sai dai wasu masu tsokanin suna zargin ya kakakin shugaban kasar ya tura sakon ne ba tare da ya karanta ba, bayan wani ya tura mishi.