✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da dalibai: An sake rufe makarantu a Kaduna

Makarantu za su ci gaba da zama a rufe sai abin da hali ya yi.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta rufe dukkannin makarantu a Jihar har sai abin da hali ya yi saboda matsalar garkuwa da dalibai.

Kwamishinan Ilimin Jihar, Mohammed Makarfi, ne ya sanar da matakin da gwamnatin ta dauka, a yayin da ake fadi-tashin kubutar da dalibai da aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren Bethel Baptist da ke jihar ta Kaduna.

“Mun nemi dalibai da su kaurace wa makarantu na tsawon mako uku, bayan haka a mako na ukun za mu sake duba lamarin mu fitar da samarwa ga jama’a da daliban,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.

Tun da farko Jihar Kaduna ta rufe makarantu na tsawon mako uku, wanda ya kare a ranar Lahadi, inji wani jami’in gwamnatin da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana da manema labarai.

Kwamishinan ce, “Umarnin da gwamna ta bayar na dakatar da bude makarantun zai ci gaba har abin da hali ya yi domin tabbatar da tsaron dalibai a duk makarantun.”

A ranar Lahadin da ta gabata, masu garkuwa da mutanen da suka afka wa makarantar kwana ta Bethel Baptist da ke Jihar Kaduna sun saki 28 daga cikin daliban da suka yi garkuwa da su.

A Litinin kuma aka samu labarin cewa wasu hudu daga cikin daliban sun tsere daga hannun masu gakuwar.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Reshen Jihar Kaduna,, Rabaran John Hayab ya ce akwai dalibai sama da 80 a hannun masu garkuwar.

Harin da aka kai a makarantar ta Bethel shi ne na 10 da ’yan bindiga ke garkuwa da dalibai a makaranta tun watan Disamban 2020 a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.

Matsalar garkuwa da dalibai domin karbar kudin fansa ya yi kamari inda sau da dama aka sace dalibai masu tarin yawa.