✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da dalibai: Mafarautan Zamfara na neman a basu gadin makarantun kwana

“La’akari da muhimmancin karatu, bai kamata a rufe makarantun ba, kamata ya yi a kare su," inji mafarautan

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya (HGN) reshen jihar Zamfara ta rubuta wasika zuwa ga Gwamnan jihar, Bello Matawalle tana neman a ba mambobinta aikin gadin makarantun kwana a fadin jihar.

A baya dai Gwamnatin Jihar ta sanar da aniyarta ta rufe makarantun kwanan dake jihar bayan ’yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai a Makarantar Sakandiren Jangebe kimanin kwanakin 10 da suka wuce.

Kwafin wasikar dai wacce aka aikewa da Ofishin Gwamnan ta hannun Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar na cewa, “Mun rubuto wannan wasikar muna rokon Gwamnan da ya amince ya ba mafarauta na asali aikin gadin dukkan makarantun gwamnati dake jihar nan.

“Mambobinmu na da jajircewa, mutane ne masu kishin kasa kuma suna da kwarewa da gogewa wajen yin aiki da sauran jami’an tsaro wajen kare yankunanmu.

“La’akari da muhimmancin daidaita zangon karatu da ma muhimmancin ilimin baki daya ga yaranmu masu tasowa ne ya sa muke ganin bai kamata a rufe makarantun ba, kamata ya yi a kare su.

“Mafarauta mutane ne dake da rijista da Gwamnatin Tarayya kuma suna da mambobi a kowanne lungu da sako na Najeriya.

“Saboda haka, tarin basirar da muke da ita ta sanin dazuka tasa muke da sha’awar bayar da gudunmawarmu wajen gadin makarantu, la’akari da muhimmancin kiyaye rayuka da dukiyoyi,” inji wasikar.

A wani labarin kuma, kwamandan mafarautan na jihar ta Zamfara, Alhaji Suleiman Lawali Zurmi ya ce matukar Gwamnatin Jihar ta amince ta basu aikin, to ko tantama babu za a iya sake bude makarantun.