✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane: Dubun wasu samari ta cika

Abokan sun hada baki suka yi karyar cewa an yi garkuwa da su

Wasu abokai da suka hada baki suka kuma yi garkuwa da kansu sun shiga hannu, an kuma gurfanar da su a gaban kotu.

An gurfanar da matasan da ake tuhma da aikata mugun laifin ne a ranar Laraba a gaban wata Kotun Majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.

Jami’in dan sanda mai gabatar da kara, Bamikole Olasunkanmi, ya bayyana wa kotun cewa matasan sun hada kai suka yi garkuwa da kansu, ne a ranar 31 ga Disamba, 2020 a Iloda, kusa da Ifaki-Ekiti a Karamar Hukumar Ido/Osi ta Jihar.

Dan sandan gabatar da kara ya roki kotun da ta dage sauraron karar don ba shi damar yin nazari a kan karar da kuma gabatar da shaidu.

Sai dai lauyoyin wadanda ake karar, sun roki kotun da ta da belinsu, inda Babbar Alkalin Kotun, Adefumike Anoma, ta amince ta kuma belin su kan kudi N50,000.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu, 2021.