✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gasar hotunan aikin naman Layyar iyali

Gasar matan da ke ganin mazajensu ko yayyensu ko kannenasu ko ’yayansu na da saukin kan da ya kamata sauran maza su yi koyi da…

Ina uwargida sarautar Mata! Da amarya ba kya laifi! Da ma duk wacce take jin mai gidanta ko yayyenta ko kannenta ko ’yayanta na da saukin kan da ya kamata sauran maza su yi koyi da su!

Ga dama kafar yada labarai ta Aminiya ta bullo da ita!

Ki dauki bidiyo ko hoton maigidanki ko yara ko ’yan uwanki suna taya ki aikin nama ki turo ta kasan wannan sanarwar.

Aminiya za ta zabi guda uku da suka fi kowanne daukar hankali ta wallafa, duniya ta gani ta shaida.

Wannan gasa an shirya ta ne domin zaburar da maza su dinga taya matayensu da ayyukan gida.

A sanya taken #ShowMeTheManAssistingYou a tare da kowane bidiyo ko hoto da aka dauka.

Barkanmu da Sallah!