✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Kofin Duniya: Qatar ta rage lokacin aiki da makarantu

Kashi hudu bisa biyar na ma'aikata za su zauna a gida, sannan makarantu za su tafi hutu saboda Gasar Cin Kofin Duniya na 2022 a…

Gwammatin Qatar na shirin rage yawan ma’aikata da za su rika zuwa aiki da kuma sa’o’in karatu a makarantu kafin da kuma a lokacin Gasar Cin Kofin Duniya da kasar za ta karbi bakunci.

A ranar Laraba Wani jami’in gwamnatin Qatar ya ce majalisar gudanarwar kasar ta rage sa’o’in aiki zuwa hudu, tare da rage yawan ma’aikatan da za su rika zuwa aiki a zuwa kashi daya bisa biyar daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa ranar 19 ga Disamba, 2022.

Daga ranar 1 zuwa 17 ga watan Nuwamba kuma lokacin halartar makarantu zai koma daga karfe 7 na safe zuwa 12 na rana, sannan a bai wa dalibai hutu daga 18 ga watan zuwa 22 ga watan Disamba.

Za kuma a hana motoci bin Babban Titin Corniche da ke makwabtaka da teku a Doha, babban birnin kasar, daga ranar 1 ga watan Nuwamba.

A halin yanzu dai ana gina masaukan magoya bayan tawagar ’yan wasan kasashe a kusa da babbar hanyar da ke birnin Doha.

Akalla mutum miliyan daya ne ake sa ran za su je kallon Gasar Cin Kofin Duniya da za a fara daga ranar 20 ga watan Nuwamba, zuwa 18 ga Disamba, 2022.

Ganin haka ne gwamnatin Qatar ta fara daukar matakan rage cunkoson ababen hawa a kan tituna masu makwabtaka da filayen wasa takwas da za a buga wasannin gasar.

Hukumomin kasar sun fi mayar da hankali a kan makonni biyu na farkon gasar, wanda a lokacin ne ’yan kallo za su fi yawa domin halartar wasannin da tawagar ’yan wasan kasashe 32 za su fafata.