✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar LaLiga: Minti 90 mafiya muhimmanci

Sakamakon wasannin da za a yi yau ne zai nuna zakarun LaLiga

A yau ne za a fafata a wasannin karshe na gasar LaLiga.

A bana, ba kamar takwarorinta na Ingila da Italiya ba, har yau da za a fafata a wasannin na karshe ba a san kungiyar da za ta lashe gasar ba.

Kungiyoyin Atletico Madrid da Real Madrid ne dai suke sa ran daga kofi.

Yayin da Atletico Madrid ke da maki 83, ita kuwa Real Madrid na da maki 81.

Atletico Madrid za ta fafata ne da kungiyar Real Valladoid wadda take kusa da ta karshe a teburi.

Idan Real Valladoid ta doke Atletico Madrid, za ta tara maki 34.

Idan aka doke Elche da Huesca, za ta iya tsira daga fadawa gasa ta biyu ta LaLiga.

Wannan ya sa aka samu rahotannin da ke nuna cewa mai kungiyar, tsohon dan wasan Real Madrid da Brazil, Dilema Ronaldo, ya yi alkawarin bai wa ’yan wasan makudan kudade idan suka lashe wasan.

Hakan ya sa Atletico Madrid ke da kalubale mai girma a gabansu.

Sai dai a wani rahoton na daban, kocin Atletico Madrid, Diego Simone, ya ce za su buga wasan ne bakin rai bakin fama domin su samu lashe gasar.

A bangaren Real Madrid kuwa, za ta fafata ne da kungiyar Villarreal, wadda ita ce ta bakwai da maki 58. Ke nan ba ta bukatar wasan sosai.

Idan su duka suka lashe wasanninsu, Atletico Madrid ta lashe gasar.

Idan su duka suka yi kunnen doki, Real Madrid za ta lashe gasar bisa la’akari da sakamakon karanwar su ta baya, wato head-to-head saboda ta doke Atletico Madrid din.

Ko ma dai yaya ne, minti 90 ne kawai anjima, amma mintuna ne kamar kwana.