✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Nahiyar Afirka: Najeriya na neman maki daya a wasa biyu

Tuni dai ’yan wasan Najeriya suka hallara tare da yin atisaye

A ranar Asabar Kungiyar Super Eagles ta Najeriya za ta fafata da kasar Benin a kokarinta na neman gurbin shiga Gasar Nahiyar Afirka ta bana.

Najeriya na neman maki daya ne kacal domin samun gurbin shiga gasar, inda take da maki 8 a yanzu a wasanni hudu da ta buga.

Benin ce ta biyu da maki 7, sai Saliyo da ke da maki 3, sai kasar Lesotho da ba ta maki ko daya.

Tuni dai ’yan wasan Najeriya suka hallara tare da yin atisaye a filin wasan Teslim Balogun da ke Jihar Legas.

Bayan wasansu na Asabar, ranar Talata kuma za su fafata da kasar Lesotho a matsayin wasan karshe a Jihar Legas.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da amincewarta na barin masu kallo 8,000 su kalli wasan Super Eagles din da za a buga a Legas, wato kimanin kashi 30 na asalin ’yan kallon da ke iya shiga filin wasan na mutum 24,000.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito cewa Najeriya ba ta ci wasa ko daya ba a bara, inda ta buga wasa hudu, ta yi kunnen doki uku, aka ci ta daya.