✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaskiyar lamari game da rashin lafiyar Maryam Yahaya

A makon jiya ne aka fara rade-radin cewa jaruma Maryam Yahaya na fama da matsananciyar rashin lafiya, batun da ya tayar da kura, musamman a…

A makon jiya ne aka fara rade-radin cewa jaruma Maryam Yahaya na fama da matsananciyar rashin lafiya, batun da ya tayar da kura, musamman a Intanet.

An yi ta rade-radin cewa asiri aka yi wa jarumar, wadansu suna cewa cuta ce da ba a sani ba, inda wannan batu ya sa wadansu suke tambayar cewa wace irin cuta ce da ba a sani, kuma hakan ya sa wadansu suka kara tabbatar da batun cewa lallai asirin aka yi mata.

Yadda lamarin ya tayar da kura a kafafen sada zumunta

A ranar Litinin da ta gabata ne fitaccen mai rubutu a Facebook, Datti Assalafy yarubutu a shafinsa, yana kira ga kungiyoyin kare hakkin mata na duniya su kawo wa Maryam Yahaya dauki, inda ya yi zargin cewa abokan sana’arta sun ruguza mata rayuwa, sannan sun mayar da ita wajen iyayenta sun kyamace ta ko ziyartarta ba sa yi.

Ya ce a rubutun, “Wannan cin zarafi ne da keta haqqin rayuwar mata dangin rauni, ba a haka ’yan Hausa fim suka dauke ta a gidan mahaifinta ba. Mahaifinta ba ya da karfin daukar lauyoyin da za su kwato mata ’yanci a biya ta diyya, tunda sun kashe mata rayuwa.”

Jarumar Kannywood Maryam Yahaya

Marubuci kuma Darakta, Jamilu Nafseen ya rubuta a Facebook a kasan wani rubutu da wani mai suna Gen Sunus ya yi cikin fushi cewa, dukkan abin da shi Datti ya fada ba gaskiya ba ne.

Shi ma shafin Dokin Karfe a Facebook ya ruwaito cewa, “Jaridar Dokin Karfe TV ita ce ta fara kawo labarin rashin lafiyar fitacciyar jarumar, wanda a sanadiyyar bullar labarin daga gare mu, wadansu sun fara yada jita-jita da labarai marasa tushe a kan asalin rashin lafiyar jarumar.

“A binciken da muka gudanar, mun sami tabbacin cewa Maryam Yahaya ta gamu da rashin lafiya wanda ake zargin asiri aka yi mata.

“Wannan shi ne hakikanin abin da ya haifar mata da rashin lafiyar da take ciki.

“Duk wani labari da wadansu za su fada a kan rashin lafiyar jarumar ba wannan ba, to ba gaskiya ba ne saboda haka jama’a su guji yada jita-jita da labarai marasa tushe da makama. Kamar yadda majiya mai tushe ta tabbatar mana, rashin lafiyarta yana da alaka ne da asiri ko jifanta da ake tunanin magauta sun yi.”

Wadannan rubuce-rubuce biyu sun ta da kura matuka, inda aka fara bibiyar asalin rashin lafiyar jarumar.

Yadda aka fara samun labarin rashin lafiyar

A ranar 19 ga Yuni ce jarumar take bikin ranar haihuwarta, yadda ta saba a duk shekara tana sanya hotuna a shafinta na Instagram, sannan ’yan uwa da abokan arziki su ci gaba da taya ta murna. Sannan takan shirya biki na musamman domin murnar.

Maryam Yahaya
Maryam Yahaya

Sai dai a bana jarumar ba ta sanya hotunan murna ba, sannan ba ta shirya bikin ba, sai da wadansu suka taya ta murna, tare da cewa Allah Ya ba ta lafiya.

Hakan ya sa aka fara tambayar abin da yake damunta. Sai kuma Sallah ta zo, inda jarumai da dama sukan nuna kwalliyar Sallah a shafukansu na sadarwa, wadansu kuma sukan je tarurrukan bikin.

A bana, Maryam Yahaya ba ta je wani taro ba, sannan ba a gan ta a sinima ba, inda ake nuna fim din Zainabu Abu na Abubakar Bashir Maishadda.

Ranar karshe da ta yi rubutu a shafinta na Instagram da Aminiya ta leka shafinta na Instagram, ta gano cewa a ranar Litinin da ta gabata, Maryam Yahaya ta wallafa addu’a a shafinta na Instagram da Larabci mai cewa, “Da sunan Allah wanda da sunanSa babu wani mai iya cutar da wani a sama da kasa, kuma Shi Mai ji ne Masani.”

A kasan rubutunta jarumai irin su A’isha Humaira da Maryam A. B. Yola da Mansur Make Up da sauransu da dama sun yi jawabi da yi mata addu’ar samun lafiya.

Ta kwana biyu tana jinya

Aminiya ta gano cewa, jarumar ta kwana biyu tana jinya amma ba a sani ba.

A shafinta na Instagram, ranar da tsohuwar jaruma Zainab Booth, mahaifiyar Maryam Booth ta rasu, Maryam Yahaya ta sanya hoton marigaiyar ta yada addu’ar samun rahama da ake yi mata, inda a kasa jaruma Amal Umar ta mayar da martani cewa, “Amin masoyiyata. Allah Ya ba ki lafiya ke ma,” kamar yadda ta wallafa a mako uku da suka gabata.

 Sannan Madam Korede ta wallafa bidiyon Maryam a shafinta, inda ta ce, “Mero Allah Ya kara sauki.”

‘Maleriya ce da Typhoid’

Aminiya ta yi kokarin gano hakikanin lamarin, inda wani mai ruwa-da-tsaki a Masana’antar Kannywood da ta tuntuba ya ce ba ya da masaniya a kan ainihin abin da yake damunta.

Sai dai wani forudusa a masana’antar ya ce maleriya da typhoid ne kawai suke damun jarumar, kamar yadda sauran mutane suke ciwo.

Da Aminiya ta ce masa ana rade-radin cewa ciwon ya yi zafi har ta koma gidan iyayenta, sai ya ce, “Haka ne. Tana gida yanzu haka.”

Aminiya ta tuntubi Maryam Yahaya

Wakilin Aminiya ya nemi Maryam Yahaya ta tarho sau uku, amma wayar tana kashe, sai dai Mujallar Fim ta ruwaito cewa jarumar tana samun sauki. Jarumar ta bayyana wa mujallar cewa: “Kowane dan Adam, Allah Yana jarabtarsa da cututtuka, ni ma Ya jarabce ni a wannan lokaci. Amma na san cewa komai yana da lokaci, sai dai masu yin yamadidi, kawai dai cuta ce daga Allah. Ni na san Allah ne Ya doro min kuma ba na zargin kowa a cikin wannan masana’anta.

“Hasali ma dai, muna zaune da kowa lafiya domin jarumai da dama sun zo duba ni; wadansu na sani, wadansu ma ban sani ba ina kwance. Ba abin da zan ce da Allah sai godiya bisa ni’imarSa.”

Game da batun Kannywood ta yi watsi da ita, jarumar ta karyata haka, inda ta ce, “Ina samun kulawa sosai, domin duk wanda ya zo za ka ga ya kawo mini wani abu da sauransu. Suna hidima da ni sosai,” kamar yadda ta bayyana wa Mujallar Fim.

A karshe ta ce, “Ina samun sauki kuma ban mutu ba kamar yadda wadansu suke yadawa, sai dai kawai yanzu ba na jin karfin jikina; kun san dai mara lafiya kan ya dawo daidai.”

Masana’antar Kannywood ta taya Maryam Yahaya ‘jinya’

Aminiya ta lura cewa kusan duk Masana’antar Kannywood ta shiga alhini, ta inda da yawa daga cikin jarumai suke ta batun jarumar ta hanyar ko dai sanya hotunanta tana nishadi tare da yi mata addu’a ko mayar da martani idan wani ya saka.