✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gawayi da icen girki sun yi tashin gwauron zabo a Taraba

Kai daya an icen girki ya koma N500, buhun gawayi kuma ya koma N2,300 daga N900

Mazauna garin Jalingo a Jihar Taraba sun koka kan yadda farashin gawayi da icen girki suka yi tashin gwauron zabo.

A halin yanzu farashin dauri daya na icen girki ya tashi zuwa N500, daga N200 da ake sayar da shi a makonnin baya.

Buhun gawayi kuma ya tashi daga N900 ya koma Naira 2,300 saboda karancinsa da kuam rashin icen girki a garin na Jalingo.

Aminiya ta gano farashin ya yi tashin gwauron zabon ne saboda matsalar tsaro da ke hana masu sana’ar shiga dazuka kafin su samar da su.

Bugu da kari an samu karuwa a yadda mutane ke yin tururuwar amfani da su a wurare daban-daban.

Wani mai sayar da ice, Malam Yakubu Sani karuwar bukatar gawayi da ice a tsakanin mazauna garin ne saboda tsadar kananzir da gas din girki.

Malam Yakubu ya kara da cewa kudin motar daukar kayan ya karu, sannan yawancin masu sannan shiga daji domin yin ice na da matukar hadari saboda ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

“Yawancin masu sana’ar tamu sun fice daga cikin dazuwa saboda rashin tsaro, wanda hakan ya sa ake famda da karancinsu,” kamar yadda ya bayyana wa wakilinmu a zantawar da suka yi.

Zubairu Hudu, mai sayar da gawayi ya ce karuwar masu neman gawayi da icen girki da kuma karancinsa ne ya sa suka yi  tashin gwauron zabo.

Ya shaida wa wakilinmu cewa masu neman gawayi daga wasu jihoihn sun karu, saboda jihohinsu sun haramta harkar icen girki ko gawayi, shi ya sa suke zuwa Jihar Taraba domin su samo.