✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Ana zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Jordan

An yi kwanaki a Jordan ana zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa.

Dubban ’yan kasar Jordan sun gudanar da zanga-zangar kin jinin mamayar da Isra’ila ke yi a yankuin Zirin Gaza na kasar Falasdinu.

Mazu zanga-zangar sun su dafifi a Amman babban birnin kasar, da kuma kusa da Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye a ranar Juma’a suna la’antar Isra’ila tare da goyon bayan Falasdinawan Kudus da Gaza.

Kusan rabin mutanen Jordan ’yan asalin Falasdin ne, baya ga Falasdinawa ’yan gudun hijira miliyan 2.2 da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa rajista a Jordan wadda a  1994 ta kulla yarjejeniyar zaman da Isra’ila.

Dandazon masu zanga-zangar sun yi ta tattaki tare da yekuwar neman ’yancin Falasdinawa da kuma jinjina wa ’yan uwansu a Gaza da Kudus

“Ya kamata a bude iyaka mu je mu kare Kudus da rayukanmu,” inji Mohammed Khalil, mai shekara 23.

Ya ce, “Ta’addanci ne abin da Isra’ila ke yi,” kuma “Shin Falasdinawa ba su da ’yancin kare kansu ne?”

Wasu mutum 3,000 sun yi cincirindo a Karameh da ke Yammacin Amman, daura da Yammacin Kogin Jordan, inda a 1968 mayakan Falasdinawa da dakarun Jordan suka gwabza fada da sojojin Isra’ila.

Rikicin Yahudawa da Falasindawa ya kara tsanani a Yammacin Kogin Jordan a ranar Juma’a bayan bangarorin biyu sun ci gaba da kai wa juna hare hare a yankin Gaza.

Hare-haren sun kashe mutane da dama, yawancinsu Falasdinawa.

Rikicin ya kazanta cikin kwana bakwai ne bayan tarzomar da aka samu a Masallacin Kudus da kuma yunkurin Isra’ila na mamaye yankunan Fadasdinawa a gabashin birnin Kudu, lamarin da ya kai ga kungiyoyin Falasdinawa mayar da martani da bakin bindiga.

An shafe kwanaki a Jordan ana gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa.