✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gbajabiamila ya yi ta’aziyyar mutuwar tsohuwar shugabar matan APC, Kemi Nelson

Tsohuwar shugabar matan ta jam'iyyar APC ta rasu a ranar Lahadi.

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana alhininsa game da rasuwar Misis Kemi Nelson, wacce ta taba zama shugabar mata ta jam’iyyar APC a yankin Kudu maso Yamma.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya bayyana marigayiya Misis Nelson a matsayin daya daga cikin ginshikan jam’iyyar APC a Jihar Legas da Najeriya baki daya, inda ya ayyana mutuwarta a matsayin babban rashi.

Ta kasance tsohuwar kwamishina a Jihar Legas kuma har zuwa rasuwarta, mamba ce a majalisar masu bada shawara ga gwamnan Jihar Legas (GAC).

Nelson, wadda tsohuwar Babbar Darakta ce ta Hukumar Inshora ta Najeriya (NSITF), ta rasu ranar Lahadi tana da shekaru 66 a duniya.