✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ghana ta zaftare albashin Shugaban Kasa saboda matsin tattalin arziki

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da zaftare kasafin kudin kasar

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da zaftare kasafin kudin kasar da akalla kashi 30 cikin 100 ciki har da rage albashin Shugaban kasa da na Mataimakinsa da na ministoci a kokarin magance matsalar da ta dabaibaye tattalin arzikin kasar.

Shugaba Nana Akufo-Addo ya ce kasar ta fada cikin matsin tattalin arziki mafi muni wanda ya tilasta dole a dauki matakan gyara don kauce wa tsanantar halin da ake ciki.

A cewar Shugabana, kasar za ta karfafa samar da kayan cikin gida tare da rage dogaro da ketare don taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin da ke cikin masassara a yanzu.

Nana Akufo-Addo ya ce ba ya ga shi kansa da mataimakinsa da ministoci da mataimakansu, wadanda zaftare albashin zai shafa su ne dukkan masu rike da mukaman siyasa a kowane mataki.

Shugaban ya ce Ghana ba ta taba samun kanta a cikin yanayin da tarin shaidanu daga sassa daban-daban suka taru tare da hada karfi don durkusar da kasar irin yanzu ba.

Nana Akufo-Addo ya ce makircin shaidanun zai zame wa kasar alfanu ta yadda za ta samar da damarmakin habaka tattalin arzikinta tare da dawo da kimar kudinta.