✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gianluca Vialli: Duniyar kwallon kafa ta sake shiga juyayi

Gianluca Vialli ya bi sahun Pele da Mihajlovic ne bayan ya dogon lokaci yana fama da cutar kansa

Duniyar kwallon kafa ta sake shiga cikin juyayi bayan rasuwar Pele da Sinisa Mihajlovic.

Sabon juyayin na zuwa ne sakamakon rasuwar tsohon dan wasan Juventus da Chelsea, Gianluca Vialli, yana da shekaru 58 a duniya.

 

Gianluca Vialli, wanda shi ma tsohon tauraro a duniyar kwallon kafa ne, ya bi sahun Pele da Mihajlovic ne bayan ya shafe dogon lokaci yana fama da cutar kansa.

Tsohon dan wasan ya wakilci Blues da Juventus da Sampdoria da kuma Cremonese a yayin da ya buga wa Italiya wasa 59.

A shekarar 2021 ce aka sake tabbatar wa da Vialli yana dauke da cutar daji a saifarsa, karo na biyu ke nan bayan da a watan Afrilun 2020 ya samu waraka daga cutar bayan shafe watanni 17 yana jinyar ta.

Ya ci gaba da harkokin kwallon kafa har a shekarar 2021, inda ya zama cikin tawagar masu horas da ’yan wasan Italiya tare da abokinsa Roberto Mancini har ta kai ga lashe gasar Euro 2020.

Rauwar Vialli

An haife Vialli a Cremona, inda ya fara wasansa tare da kungiyar Cremonese kuma ya taimaka musu su ci gaba har zuwa samun gurbin shiga gasar Serie B.

Hakan ne ya ba shi damar jawo hankalin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Italiya.

Yayin da tauraruwarsa ta nuna alamar haske, kungiyar Sampdoria ta yi gaggawar daukar sa a shekarar 1984.

Shi da abokinsa Mancini sun rika nuna bajinta, har aka yi musu lakabi da Tagwayen Masu Jefa Kwallo a yayin da suka taka rawar gani har kungiyar ta yi nasarar lashe gasar Serie A a kakar 1990-1991.

Har ila yau, Vialli ya lashe Kofin Italiya uku da Gasar Kofin Turai a kungiyar ta Sampdoria, sannan ya kai wasan karshe na Kofin Turai a 1992.

Daga baya ya kafa kafa tarihin zama dan wasa mai tsadar gaske da aka saya a kan Fam miliyan 12.5 yayin tafiyarsa Juventus.

Ya lashe gasar Serie A, Kofin Italiya da Kofin Zakarun Turai a Turin, sai dai mafi daukar hankali a tsawon shekaru hudun da ya shafe a Juventus, shi ne lokacin da kungiyar ta lallasa Ajax a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai a shekarar 1996.

Horas da ’yan wasa

Ruud Gullit ya yi zawarcin Vialli zuwa Chelsea kuma ya samu nasara a 1996, a wani yunkuri na karfafa kungiyar ta Stamford Bridge, tare da mai horar da ’yan wasa na Italiya a 1998 yana da shekaru 33 lokacin da aka sallamin kociyan na Holland daga aikinsa.

Vialli ya jagoranci Blues zuwa samun nasarar lashe Kofin Lig din Ingila da Kofin Kalubale, kuma ya yi ritaya daga taka leda a 1999 tare da barin kulob din bayan jefa kwallaye 259 a cikin wasanni 673.

A lokacin da yake koci, Vialli ya taimaka wa Chelsea ta lashe kofin FA a wasan karshe da aka buga a tsohon filin wasa na Wembley a shekara ta 2000, amma daga bisani kungiyar ta kore shi bayan wasanni biyar kacal da soma kakar 2000-2001

Ya shafe dan gajeren lokaci a matsayin koci a Watford a lokacin kakar 2001-02, amma ya mai da hankalinsa ga ilimin kimiyya bayan ya bar Vicarage Road.

A matakin kasa da kasa, Vialli ya buga wa Italiya wasanni 59, inda ya ci kwallaye 16. An sanya sunan shi a cikin tawaga mafi bajinta a gasar Euro 88 kuma ya taimaka wa Italiya zuwa wasan kusa da na karshe a Gasar Kofin Duniya da kasar ta karbi bakunci a 1990.