✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gidajen burodi sun shiga yajin aiki a Filato

Masu sana'ar sayar da shayi da sun rufe wuraren sana'ar tasu saboda karancin burodi.

Masu gidajen burodi a Jihar Filato sun shiga yajin aikin kwana uku saboda tsadar Fulawa.

Yajin aikin an fara shi je a ranar Talata don nuna rashin goyon baya kan yadda kayan masarufi ke tashin gwauron zabi.

Aminiya ta rawaito cewa gidajen burodi da dama a jihar sun tsunduma yajin aikin, galibi saboda tashin farashin fulawa wadda ita ce jigon wajen hada burodin.

Amma da wakilinmu ya tuntubi Sakataren Kungiyar Masu Gidajen Burodi na Kasa, Salis Abdullah a kan lamarin, ya musanta shiga yajin aikin.

Ya ce an kulle gidajen burodin ne domin su tsaftace su zuwa wani lokaci.

Sai dai daya daga cikin mambobin kungiyar ya tabbatar da cewa sun shiga yajin aikin, kuma za su kara farashin burodi.

Wakilinmu ya zagaya wasu wuraren da ake sayar da burodi don gane wa idonsa yadda ta kaya, kuma ya iske akwai karancinsa a wuraren.

Wasu daga cikin masu sana’ar shayi, sun rufe wuraren sana’ar tasu saboda a cewarsu ba za su iya sayar da shayi babu burodi ba.