✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidajen karuwai sun nemi kotu ta shiga tsakaninsu da hukuma

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya ta dage sauraran karar da masu gidajen giya da na karuwai suka kai karamar hukumar…

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya ta dage sauraran karar da masu gidajen giya da na karuwai suka kai karamar hukumar Sabon Gari ta jihar.

Masu karar na neman kotun ta dakatar da yunkurin hana su sayar da giya da harkokin gidajen badala a karamar hukumar.

Kotun wadda mai shari’a Kabir Dabo ke jagoranta ta dage sauraran shari’ar bayan da lauyoyin bangarorin suka gabatar da bayanansu.

Bayan fitowa daga kotun, lauyan masu kara Barista Solomon Kaine ya ki cewa komai saboda maganar tana gaban kotu.

A nasa bangaren, lauyan Karamar Hukumar Sabon Garin, Barista Shamwilu Muhammad Nasir ya ce masu karar ba su bayar da sanarwar kwana 30 da doka ta shardanta ba.

A cewarsa, doka ce ta sashi 179 ga duk wanda zai yi karar shugaban karamar hukuma ya yi hakan.

“Sashin doka na shekarar 1999 ya yi bayanin cewa, duk wanda zai yi karar shugaban karamar hukuma zai kai takardarsa ne ga sakataren karamar hukuman, wanda ba su yi haka ba”, inji shi.

A yanzu haka dai kotun ta dage sauraren karar da aka shigar.