✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya ta raba wa Marayu 400 kayan Sallah a Ajingi

Gidauniyar tallafawa Marayu ta Karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano, ta gwangwaje marayu 400 maza da mata da kayan Sallah a cibiyar musulunci ta karamar…

Gidauniyar tallafawa Marayu ta Karamar Hukumar Ajingi a Jihar Kano, ta gwangwaje marayu 400 maza da mata da kayan Sallah a cibiyar musulunci ta karamar hukumar da ke garin Ajingi.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar Malam Habibu Ajingi, ya yi matukar nuna godiyarsa ga Allah (S.W.T), ya kuma jinjinawa al’ummar da suka tallafawa gidauniyar ta samu damar gudanar da wannan aikin lada.

Ya ce an kafa wannan gidauniyar ce a shekara ta 2010 da kimanin mambobi bakwai domin tallafawa Marayu

Malam Habibu, ya kara da cewar suna samar da kudin da suke tallafawa ne ta hanyar kafawa kowanne mamba haraji na wani kaso da zai bayar sannan suna neman tallafin al’umma idan bukatar hakan idan ta taso.

Ya kuma bayyana nasarorin da suka samu, ciki har da sanya marayu a makaranta suna kuma kula da lafiyarsu da kuma tallafa musu da kayan Sallah.

Wani sashe na marayu maza
Wani sashe na marayu
Wani sashe na marayu mata
Yayin da ake mika wa wani maraya kayan sallah
Kayan sallar da aka raba wa marayun

Kazalika, ya kuma ce wannan kungiya tana da babban fili mallakinta da take son ginawa marayun makaranta da kuma masana’anta domin su dogara da kansu.

A nasa jawabi, dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Ajingi a Majalisar Dokokin Jihar Abdul’aziz Garba Gafasa da ke zaman Walin Gaya, ya yaba wa wannan gidauniya ta marayu dangane da yadda suke nemawa marayu ingantacciyar rayuwa.

Garba Gafasa, wanda ya samu wakilcin daya daga cikin hadimansa Malam Ya’u Sunusi, ya tabbatar musu da cewa kofar dan majalisar kullum a bude take don ba da tasa gudunmawar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Wakilai daga kungiyar marayu ta garin Wudil, suma sun yi kira da ’yan siyasar Karamar Hukumar Ajingi da masu hannu da shuni da sauran al’ummar gari da cewa suna tallafawa marayu ta kowacce hanya.

A nasa bangaren, Sardaunan Ajingi, Alhaji Labaran El- Mahamoud Ajingi, ya ja hankalin jama’a da cewa, shi tallafi ba wai sai ka wadata za ka iya bai wa marayu ba, a’a dan abin da kake da shi za ka iya tallafawa, domin yin hakan yana da matukar falala gami da samun alheri mai dorewa duniya da lahira.”

Haka kuma, Shugaban Karamar Hukumar Ajingi, wanda kansilan mazabar Dundun ya wakilta, Alhaji Ubale Ya’u, ya yi kira ga marayun da su kasance masu juriya da hakuri.

Ya kuma kara da cewar suma a shirye suke su tallafawa wannan kungiya, inda ya yi wa kungiyar addu’ar samun ci gaba tare da fatan alheri.