✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Zakkah da Wakafi ta koya wa ’yan mata 90 sana’oin hannu a Gombe

An zabo masu cin gajiyar shirin ne ta hanyar bai wa makarantun Islamiyya gurabe su kawo wadanda za a koya wa sana'o'i.

Gidauniyar Zakka da Wakafi ta Jihar Gombe ta yaye ’yan mata 90 da ta ba wa horo kan sana’o’in hannu daban-daban domin dogaro da kai.

Shugaban Gidauniyar, Ustaz Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce ’yan mata masu shekara 15 zuwa 25 ne aka koya wa sana’o’in domin sama musu madafa a rayuwarsu, a kokarin gidauniyar na samar da ayyukan yi da kuma rage zaman kashe wando.

Ya bayyana cewa 31 daga cikin ’yan matan sun koyi hada kayan kamshi ne, 10 sun koyi hada sarka da awarwaro, wasu 10 kuma suna hada jakukkuna da takalma, sai wasu 10 da suka koyi saka, sauran kuma dinki.

Ya kara da cewa an zabo ’yan matan da suka ci gajiyar shirin ne ta hanyar bai wa makarantun Islamiyya gurabe su kawo wadanda za a koya wa sana’o’i.

Abdullahi Lamido ya bayyana cewa sana’oin za su inganta rayuwar ’yan matan ta hanyar samar musu kudaden shiga da za su kyautata rayuwarsu,

An yaye matan ne bayan sun share makonni biyu suna koyon sana’o’in, sannan za a bai wa kowacce daga cikinsu jarin N10,000.

Lamido, ya ce idan al’umma za su tallafa, gidauniyar za ta koya wa dubban mata sana’oi iri-iri, da za su rage musu zaman banza.

Daga nan sai ya yi kira ga al’umma da su taimaka wa gidauniyar wajen cimma burinta na rage talauci a tsakanin jama’a.

Wasu daga cikin matan da suka ci gajiyar shirin sun yaba wa gidauniyar suna masu cewa yana da kyau gwamnati ta shigo ciki wajen ba da nata gudumawar.

Wata wacce ta ci gajiya, Hadiza Mohammad, wadda ta koyi sana’ar saka ta jinjina wa gidauniyar, inda ta ce sana’ar za ta ci gaba da yi domin zai taimake ta har gidan aure.

Sannan ta yi kira ga gwamnati da ta dinga tallafa wa kungiyoyin da suke taimakon al’umma irin su Gidauniyar Zakka da Wakafi.

Malama Maimuna Haladu da ta koyi hada turaren kamshi da man shafawa ta ce da za a samu irin wadannan kungyoyi guda uku a Gombe, to da za a rage talauci sosai a tsakanin al’umma.