✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Gini ya rufta kan lebura a Legas

Ginin ya rufta kan wani lebura yayin da yake tsaka da aiki.

An tabbatar da mutuwar wani lebura yayin da wani gini ya rufta kansa a yankin Aromire da ke tsakiyar Ikeja a Jihar Legas.

Ginin mai hawa daya wanda ake aikin gyaransa ya rushe sannan ya danne wasu leburori da ke aikinsa.

An ruwaito cewar ginin ya kasance yana dauke da wata shahararriyar kasuwar sayar da mota a yankin.

A cewar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), “Ma’aikatan da ba su da kwarewa ne ke gudanar da aikin, wanda ya haifar da rugujewar wani bangare na ginin.”

Sakataren LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa wani ma’aikaci daya ne ya rasa ransa yayin da wasu suka ji rauni

Ya ce, “Binciken da aka gudanar ya nuna cewa ginin ba shi da wata alamar rushewa.”

A halin da ake ciki an rufe ginin yayin da hukumar kula da gine-gine ta jihar (LASBCA) da ‘yan sanda za su ci gaba da gudanar da bincike.