✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasa mai karfin maki 6.6 ta afka wa China

Kawo yanzu dai ba iya tantance girman barnar da girgizar kasar ta janyo ba.

Wata girgizar kasa mai karfin maki 6.6 ta afku a Kudu maso Yammacin kasar China a Litinin din nan a cewar Cibiyar Binciken Yanayin Kasa ta Amurka USGS.

USGS ta ce girgizar kasar ta afku a nisan kilomita 43 da kuma zurfin kilomita 10 a Kudu maso Gabashin birnin Kangding da ke lardin Sichuan.

Kawo yanzu dai ba iya tantance girman barnar da girgizar kasar ta janyo ba kuma babu wani rahoto da ya nuna an samu asarar rayuka.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito wani mazauni na cewa an dai ji girgizar kasa cee a babban birnin Chengdu mafi kusa da Kangding.

“Na ji girgizar sosai,” a cewar wata mata mai suna Chen. “Wasu makwabta na a kasa su ma sun ce sun ji girgizar sosai.”

Girgizar kasa kusan dai za a iya cewa ta zama ruwan dare gama gari a kasar Sin, musamman a Kudu maso Yammacin kasar mai yawan fama da ita.

Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka jikkata bayan girgizar kasa guda biyu da suka auku a Kudu maso Yammacin China a watan Yuni.

A wancan lokaci, girgizar kasa mai karfin maki 6.1 ta afku ne a wani yanki mai jama’a kalilan da ke da tazarar kilomita 100 daga Yammacin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan mai yawan jama’a miliyan 21.

Bayan mintuna uku ne aka yi wata girgizar kasa mai karfin maki 4.5 a wata Gunduma da ke kusa da inda aka samu asarar rayuka da jikkatar mutane.

A shekarar 2008 ne wata girgizar kasa mai karfin maki 8.0 ta auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan wadda ta yi sanadiyar dubun-dubatar mutane.