✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 26 sun rasu a gida daya a girgizar kasa a Afghanistan

Matan aure da kananan yara na daga cikin mutum 26 da rufin gini ya fada a kansu

Akalla mutum 26 ne aka tabbatar da rasuwarsu a gida daya a sakamakon wata girgizar kasa mai karfin maki 5.3 a kasar Afghanistan.

Mutanen sun gamu da ajalinsu ne bayan rufin gidansu ya rufta a kansu a yankin Qadis da ke Yammacin Lardin Badghis na kasar.

“Matan aure biyar da kananan yara hudu na daga cikin mutum 26 da suka rasu a girgizar kasar,” a cewar mai magana da yawun Lardin Badghis, Baz Mohammad Sarwary.

Ya ce girgizar kasar ta kuma lalata wasu gidaje a gundumar Muqr da ke cikin Lardin, sai dai ba a kai ga samun alkaluman wadanda lamarin ya shafa a yankin ba tukuna.

Yankin Qadis dai na daga cikin yankunan da matsalar karancin ruwan sama ta fi yi wa illa a kasar Afhganistan, kuma ta yi ta fama da rashin kayan agaji daga kasashen duniya a tsawon shekara 20 da suka gabata.

Kasar Afghanistan dai na yawan fama da girgizar kasa, musamman a yankin da Tsaunin Hindu Kush yake, wanda ke kan iyakokin kasar da nahiyar Turai da kuma Asiya ta bangaren Indiya.

A halin yanzu kasar na fama da matsananciyar rayuwa na yunwa da hauhawar farashin kaya, tun a watan Agustan 2021 da Taliban ta kwace ikon kasar, wanda ya sa kasashen duniya rufe asusun ajiyar kasar da ke kasashen ketare.

Girgizar kasa na yin gagarumar illa ga gidaje marasa inganci musamman na talakawa irin na Afghanistan.

A shekarar 2015, kusan mutun 280 ne suka rasu a wata girgizar kasa mai karfin maki 7.5 a yankin Kudancin Asiya, yawancin mace-macen a kasar Pakistan, makwabciyar Afghanistan.

A lokacin iftila’in ne aka mutsuke wata karamar yarinya mai shekara 12 a Afghanistan, a lokacin da dalibai suke turmutsutin neman tserewa daga ginin makarantarsu da ke neman faduwa a girgizar kasar.