✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasa ta yi ajalin fiye da mutum 240 a Turkiyya da Syria

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afka wa yankunan da ke iyakar kasashen biyu.

Wata kakkarfar girgizar kasa ta kashe fiye da mutane 240 a kasashen Turkiyya da Syria.

Girgizar kasar wadda ta afka wa kasashen a safiyar wannan Litinin din ta rushe gidaje bila-adadin.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa akwai fargabar ibtila’in ya shafi wasu yankuna na tsibirin Cyprus da Masar.

Sanarwar Ma’aikatar Lafiyar Syria ta bayyana cewa mutum 237 girgizar kasar ta kashe a iya yankunan da ke karkashin kulawar gwamnati.

Haka kuma ta ce akwai wasu mutum 639 da suka jikkata yayin da bayanai ke cewa a yankunan ’yan tawayen Kurdawa ibtila’in ya kashe mutane kusan 10.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afka wa yankunan da ke iyakar kasashen biyu.

Kazalika, ta shafi yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin Syria da suka kunshi Aleppo da Alatakia da Hama da kuma Tartus, lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar ta tsallaka tsibirin Cyprus da kuma Masar.

Kuma an jiyo ruguginta har daga Gaza. An kuma samu rushewar gidaje a Lebanon.

Tun da misalin karfe 4 na asubahi girgizar kasar ta dirarwa yankunan Gazantep mai yawan jama’a miliyan 2 a Turkiya.

Hukumar Kula da Bala’o’i ta kasar na cewa yanzu haka an zakulo gawarwakin mutane 76 kodayake akwai yiwuwar gano tarin mutane a baraguzan gine-ginen da girgizar kasar ta rushe.

Tuni kasashen Duniya suka fara mika wa kasashen biyu tayin kai musu dauki ciki har da Amurka da ta ce a shirye take ta kawo dauki ga wadanda ibtila’in ya shafa.

Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya ya sanar da aike jami’ai na musamman don bayar da kulawa da kuma aikin ceto wadanda ibtila’in ya rutsa da su.

Turkiyya dai ta ayyana dokar ta baci tare da kira ga mutane su dakatar da amfani da wayoyinsu, saboda masu aikin agaji su samu damar kai wa ga wadanda suka makale a cikin baraguzai.

A 1999, irin wannan mummunar girgizar kasar ta yi ajalin mutane dubu 17.