✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasa: Yawan wadanda suka rasu a Turkiyya da Siriya sun haura 2,300

Masu aikin ceto na ci gaba da bincike don gano wadanda lamarin ya rutsa da su

Kawo yanzu, rahotanni sun ce yawan wadanda suka mutu a girgizar kasar da ta auku a kasashen Turkiyya da Siriya ranar Litinin sun haura 2,300.

Girgizar kasar wanda karfinta ya kai 7.8, ta lalata galibin biranen Turkiyya a yankunan da a nan galibin ’yan gudun hijira daga Siriya suke da zama.

Shugaban Cibiyar Kula da Girgizar Kasa na Kasar Siriya, Raed Ahmed, ya ce “Wannan ita girgizar kasa mafi karfin da cibiyar ta taba gani a tarihinta.”

An ga masu aikin ceto na ta kokarin bincike domin gano mutane da kasa ta rufta da su, walau a raye ko a mace.

Akalla mutum 810 aka ce sun mutu Siriya, sannan 1,498 a Turkiyya kamar yadda jami’au suka bayyana.

Kafin wannan lokaci, girgizar kasa mafi muni da Turkiyya ta gani ita ce wadda ta auku a 1939 inda mutum 33,000 suka mutu.