✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girman hannuwa da kafafu ya shigar da wa da kanwa a kundin tarihi na duniya 

A koyaushe ina mafarkin sanya tufafi kamar sauran mata.

Wadansu ’yan uwa biyu wa da kanwa a kasar Masar, sun samu lambar Kundin Tarihi na Duniya ta Guinness World Records, bayan auna girman hannuwa da kafafunsu da fadin hannuwan hagu zuwa dama.

Mohamed Shehata mai shekara 34 da Huda Shehata mai shekara 30, duk sun samu wani yanayin sauyin halitta ne da ya haifar musu da haka.

Kafin su balaga ne hakan ya faru saboda wani ciwo, wanda yake haifar da kwayoyin hilittarsu su rika girma.

Yanzu haka Mohamed yana rike da lambar kundin tarihi ta Guinness World Records guda biyu, wanda hakan yake nufin shi ne mafi girman hannu da kuma kafa a kan duk wani namiji mai rai a duniya.

Mohamed Shehata
Huda Shehata da mahaifiyarta
Huda Shehata a lokacin da ake auna fadin hannunta na hagu zuwa dama

An auna hannunsa na hagu yana da tsawon inci 12.32, kuma tafin hannunsa yana da tsawon kafa 8 da inci 2.5.

Huda Shehata kuma tana rike lambar Kundin Tarihi na Duniya da bayanan da suka nuna cewa ita ce mace mafi girman hannuwa da fadin hannuwa a kan duk wata mace mai rai.

An auna kafarta ta dama tana da tsawon kafa 1 da inci 1.02; hannunta na hagu kuma an auna shi yana da tsawon inci 9.56; sannan an auna tafin hannunta an gano yana da tsawon kafa 7 da inci 8.4.

Idan an hada tsawon ’yan uwan biyu, suna da tsawon kafa 13 da inci 7, kusan tsawon bas mai hawa biyu.

Kuma har yanzu suna kara tsawo, duk da haka suna da bukatar a yi musu tiyata don dakatar da ci gaban tsawon da suke yi, saboda hakan yana iya zama hadari ga lafiyarsu.

“A koyaushe ina mafarkin sanya tufafi kamar sauran mata, amma zan ci gaba da rayuwa da yanayin sauyin halittata da kuma gamsuwa da yadda rayuwata take,” kamar yadda Huda Shehata ta bayyana wa jami’an ba da kyautar lambar Kundin Tarihi na Duniya.