✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Giwaye na barazana ga noman abinci a Borno

Giwaye na neman zama barazana ga mutanen yankin Kala-Balge dake jihar Borno.

Wani garken giwaye na barazana ga noman abinci a garin Kala-Balge da ke Jihar Borno.

Giwayen kusan 250 sun tsallako daga kasar Chadi suka ratso ta Kamaru, sannan suka fara rayuwa a garin Kala-Balge.

Babagana Shettima wanda shugaba ne a Kala-Balge, ya ce, “Mutane suna cikin wahala, da yawansu suna zaune ne a sansanin ‘yan gudun hijira.

“Dole ne su yi noma domin su samu abin da za su ci amma giwaye sun cika gonakin da suke noman”, inji shi.

Akalla mutum 8,000 ne daga Kala-Balge ke ci gaba da zama a sansanin ‘yan gudun hijira saboda gudun ta’addacin ‘yan Boko Haram.

Shettima ya kara da cewa sai mutanen Kala-Balge sun yi tafiyar mil 12 a kullum zuwa iyakar Kamaru domin sayen abinci.

Hare-haren Boko Haram ya sa giwaye ya da zango yankin domin ci gaba da rayuwa.

Kafin watan Oktoba, an yi hasashen akwai giwaye 300 dake rayuwa a dazuka daban-daban a fadin Najeriya.

Hare-haren Boko Haram a yankin Tafkin Chadi ya tilasta wa mutane sama da miliyan biyu yin hijira daga gidajensu domin tsira da rayuwarsu.