✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Giwaye sun addabi manoma a Borno

Yanzu gaba daya garin da daddare za mu fita mu kona tayu, muna kade-kade don mu kore su.

Rahotanni sun bayyana cewa giwaye sun addabi manoma a yankin Gamboru Ngala na Jihar Borno da ke da iyaka da Kasar Kamaru.

Manoman sun yi kira ga hukumomi da su kai musu dauki saboda barna da giwaye suke yi wa gonakinsu a yankin.

Bayanai sun yi nuni da cewa giwayen sukan far wa gonakin mazauna yankin ne da tsakar dare su cinye musu amfanin gonakinsu.

“Gaskiya ba zan iya ce maka ga yawan giwayen nan ba. Yanzu gaba daya garin da daddare za mu fita mu kona tayu, muna kade-kade don mu kore su,” a cewar Alhaji Katomi, daya daga cikin mazauna yankin.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa, ire-iren kayan amfanin gona da suke lalatawa sun hada da dawa, wake da sauran shuke-shuke a cewar mazauna yankin.

“Rokonmu shi ne gwamnati ko hukumomi masu zaman kansu, su tallafa mana,” in ji Alhaji Abba Greman Ngala.

Hadimi na musamman ga Gwamnan Jihar Borno, Abdulrahman Abdulkarim, wanda ya fito daga yankin na Gamboru Ngala, ya ce sun samu labarin wannan lamari kuma suna kokarin duba yadda za su magance wannan matsala, domin wannan ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa ba.