✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara a haramtacciyar matatar mai ta kashe sama da mutum 100 a Imo

Galibin mutanen da suka kone dai ma’aikatan matatar ne

Sama da mutum 100 ne ake fargabar sun kone kurmus bayan wata gobara ta tashi a wata haramtacciyar matatar mai da ke dajin Abaezi na Karamar Hukumar Ohaji-Egbema a Jihar Imo.

Wasu motoci guda shida kuma sun kone kurmus yayin gobarar wacce ta tashi da daren Juma’a, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

Sai dai Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) reshen Jihar, Ifeanyi Nnaji, ya ce bisa rahoton da suka samu, mutanen da suka mutu ba su wuce 20 ba.

Shi kuwa Kwamishinan Albarkatun Man Fetur na Jihar, Goodluck Opiah, ya ce sun gano mamallakin haramtacciyar matatar, amma ya riga ya cika wandonsa da iska.

Sai dai ya ce tuni ’yan sanda suka bayyana shi a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo.

Shugaban Kungiyar Matasan yankin na Egbema, Okenya Theadus Mario, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilinmu.

Ya ce lokacin da ya isa wajen, ya iske ana ta debo sassan gawarwakin da suka kone a wajen, wadanda galibi na masu aiki a matatar ne da kuma na abokan cinikinta.

Shi ma Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, CSP Mike Abatham, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin abin takaici.