✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara a tashar nukiliya; fararen hula na barin biranen da Rasha ta kwace

Sabbin abubuwan da suka faru a yakin Rasha a Ukraine

A safiyar Asabar sojojin Rasha suka fara ba fararen hula damar ficewa daga wasu manyan birane biyu na kasar Ukraine inda sojojin suka jima suna luguden wuta.

A yayin da yakin Rasha da Ukraine ke ci gaba, gobara ta tashi a tashar makamashin nukiliya ta biyu da sojojin Rasha suka kwace a kasar.

Ga sabbin ci gaban yakin Rasha a Ukraine:

– Formula 1: An dakatar da dan tseren motar Rasha –

A safiyar Asabar kungiyar tseren mota ta Haas a gasar Formula One ta sallami direbanta dan kasar Rasha, Nikita Mazepin, tare da soke kwantiraginsu da mai daukar nauyin gasar Uralkali nan take, saboda mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

– Gobarar tashar nukiliya –

An kashe wata gobara da ta tashi a tashar makamashin nukiliya mafi girma a nahiyar Turai da ke Zaporizhzhia, inda Ukraine ta zargi Rasha da “ta’addancin nukiliya”.

Daga baya sojojin Rasha sun karbe tashar nukiliyar ta Zaporizhzhia wadda ita ce ke samar da kashi daya bisa biyar wutar lantarkin Ukraine, bayan da jami’an kashe gobara suka ce an hana su kaiwa ga gobarar na tsawon sa’o’i.

– Rasha ‘mahaukaciya ce’ —West –

A wani taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Jakadiyar Amurka, Linda Thomas-Greenfield, ta ce harin ‘rashin hankali’ da Rasha ta kai a cikin dare na mummunar barazana ga daukacin kasashen Turai da ma duniya baki daya.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na Rasha, Vassily Nebenzia, ya musanta cewa sojojin kasarsa sun yi ruwan wuta a masana’antar nukiliyar, yana mai cewa kalaman ‘kanzon kurege ne’.

– IAEA ta yi tayin zuwa Ukraine –

Babban Daraktan Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya yi tayin tafiya zuwa Ukraine domin tattaunawa da ita da Rasha kan tabbatar da tsaron cibiyoyin nukiliya.

– Tsagaita wuta a birane biyu –

Ma’aikatar Tsaron ta Rasha ta sanar da tsagaita bude wuta domin bai wa fararen hula damar ficewa daga garin Volnovakha da kuma birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa, bayan dakarun Rasha sun yi wa birnin kawanya.

Magajin Garin Mariupol, Vadim Boychenko, ya ce za a fara kwashe mutanen da karfe 9 na safe agogon GMT (karfe 10 na safe agogon Najeriya).

Babban birnin na Mariupol mai mazauna 450,000 da ke kan Tekun Azov na da matukar mahimmanci.

Birnin wanda ya sha luguden atilaren sojojin Rasha, ya kasance ba tare da wutar lantarki, abinci, ruwa ba ko kayan dumi na tsawon kwanaki a cikin zurfin hunturu a sakamakon yakin.

– An shirya karin tattaunawa –

Daya daga cikin masu shiga tsakani na Ukraine ya ce a karshen wannan mako ne ake shirin gudanar da zagaye na uku na tattaunawa tsakanin kasarsa da Rasha kan kawo karshen fadan.

Shugaban Rasha Vladimir Putin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugabar Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce Rasha a shirye take ta tattauna kan Ukraine idan an biya dukkan bukatunta.

– Barazanar kurkuku ga ’yan jarida –

Kafar yada labarai ta BBC ta ce ta dakatar da ayyukan ’yan jaridanta a Rasha bayan Shugaba Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ta tanadi tsttsauran dauri kan yada “labaran karya” game da yakin.

Kazalika jaridar Novaya Gazeta ta Rasha da ta lashe lambar yabo ta ce za ta daina bayar da rahotanni kan yakin.

– ‘Ba yanzu ba’ –

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya yi gargadin cewa yakin Ukraine ba zai kare nan kusa ba, kuma dole ne kawayen Amurka da na Turai su ci gaba da matsa lamba kan Rasha har sai an kawo karshen yakin.

– G7 na barazanar kara takunkumi –

Ministocin harkokin wajen kasashen G7 sun yi gargadin cewa Rasha za ta kara fuskantar takunkumai masu tsanani saboda mamaye Ukraine.

Sun kuma yi kira ga fadar Kremlin ta Rasha da ta dakatar da kai hare-hare a kusa da tashoshin makamashin nukiliya.

– NATO ta ki ta hana shawagin jirage –

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya ce kawancen ba zai sanya dokar hana shawagin jiragen sama a Ukraine ba.

Ya bayyana haka ne bayan Shugaban Kasasr Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bukaci a taimaka a dakatar da harin bam da Rasha ke kai wa a kasarsa.

– Rasha: Saniyar ware –

Rasha ta kara zama saniyar ware fiye da kowane lokaci bayan kuri’ar tarihi a Kwamitin Kare Hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya domin gudanar da bincike kan cin zarafin da aka yi a lokacin yakin Ukraine. A lokacin taron, kasar Eritrea ce kawai ta goyi bayan Rasha.

– An kashe mutum 47 a Arewacin Ukraine –

Hukumomin yankin Chernihiv da ke Arewacin kasar Ukraine sun ce mutun 47 ne suka mutu sakamakon wani hari da jiragen saman Rasha suka kai a birnin.

– Yawaitar fyade a Kyiv –

Ministan Harkokin Wajen kasar Ukraine ya yi ikirarin cewa an samu “kararraki da dama” cewa sojojin kasar Rasha suna yi wa matan Ukraine fyade tare da yin kira da a kafa kotun kasa da kasa kan laifukan yaki.

– Mutum miliyan 1.2 sun tsere –

Sama da mutane miliyan 1.2 ne suka tsere daga Ukraine zuwa kasashe makwabta tun bayan da Rasha ta mamaye ta makon da ya gabata, inji Majalisar Dinkin Duniya.

– Mai da iskar gas sun hau, hannunayen jari sun fadi –

Kasuwannin hannun jari na duniya sun fadi, a yayin da farashin iskar gas ya kai wani matsayi mai daraja.

Farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabo a yayin da masu zuba jari ke fargabar barazanar da na iya karuwa bayan Rasha ta kai hari kan tashar nukiliya a Ukraine.

– Barazanar yunwa –

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da matsalar karancin abinci da ke kunno kai a yankunan da ake fama da rikici a Ukraine.

Ta bayyana cewa a tashe-tashen hankulan da ake samu a harkar noma da fitar da amfanin gona zuwa kasuwanni na iya haifar da karancin abinci a duniya.