✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara: An kubutar da mutum 111 da N180m a Kano

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta yi nasarar kubutar da rayukan akalla mutum 111 da dukiyoyin jama’a da suka kai kimamin Naira miliyan 180.2…

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta yi nasarar kubutar da rayukan akalla mutum 111 da dukiyoyin jama’a da suka kai kimamin Naira miliyan 180.2 a ibtila’in gobara 95 da suka auku cikin Jihar a watan Fabrairun da ya gabata.

Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar, Alhaji Sa’idu Muhammad ne ya bayyana alkaluman a wata sanarwa da ya gabatar a ranar Laraba cikin kwaryar birnin Dabo.

Kakakin hukumar, ya kuma ce an samu salwantar rayuka takwas da asarar dukiya ta kimanin Naira miliyan 11.3 da gobora ta lankwame.

“An kubutar da mutane 59 ta hanyar kiran wayar salula, sai guda 13 da mazauna yankin suka gaza sanar da mu,” in ji shi.

Muhammad, ya bayyana cewa galibin ibtila’in gobarar da suka auku a Jihar na da alaka ne da sakaci kan kula da tukunyar girki ta gas da wadanda suka shafi na’urorin da ke amfani da wutar lantarki.

Ya shawarci mazauna Jihar a kan kodayaushe su zama masu kiyaye wa da lamarin wuta saboda gudun abin ka iya zuwa ya dawo.