✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: An yi asarar rayuka 166 a Kano a bara

Da dama daga gobarar da aka samu a shekarar sanadiyar iskar gas ce.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce mutum 166 ne suka rasu, sannan kuma an yi asarar dukiya ta Naira miliyan 358 da ta kone a shekarar 2022 da muka yi bankwana da ita.

Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa mutum 1,035 da dukiyar da ta kai kwatankwacin Naira miliyan 905 suka ceto a shekarar.

“Mun samu kiraye-kirayen gaggawa 736, da kuma wasu na jabu 208 a 2022.

“Mun kai dauki wurare 575 da aka samu hatsari a jihar, sai kuma dabbobi 6 da su ma muka ceto su a shekarar.

Abdullahi ya kuma ce da dama daga gobarar da aka samu a shekarar sanadiyyar iskar gas ce, da kuma amfani da kayayyakin lantarki marasa inganci.

Ya shawarci al’umma a wannan lokaci na sanyi, da su tabbatar sun kashe wutar jin dumi da wadataccen ruwa, gudun tashin gobarar.