✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: An yi asarar rayuka 7 da kadarorin Naira miliyan 112 a Bauchi

Hukumar ta ce ta ceto mutane da dama tare da tseratar da dukiyoyin al'umma a jihar.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Bauchi, ta ce an yi asarar rayuka bakwai da dukiya ta kimanin Naira miliyan 112.5 a gobarar da aka samu a jihar daga watan Yuli zuwa Satumba, 2022.

Hukumar ta ce ta kuma ceto rayuka 46 da dukiya ta kimanin Naira miliyan 265.2 a cikin gobara 66 da aka samu a hukumance a tsawon wannan lokaci.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata kididdigar gobara da kakakin hukumar, Mista Abubakar Bala, ya fitar a ranar Laraba a Bauchi.

Ya ce bayanan sun kunshi alkaluman gobarar da aka samu a cikin gidaje da masana’antu.

A cewarsa, hukumar ta samu kiraye-kirayen neman agajin gaggawa guda 38 sakamakon tashin gobara a gidaje.

Ya ce hukumar cikin wata biyun da suka gabata, ta samu kiraye-kiraye 23 na neman agaji inda ta ceto rayukan mutum 14.

Kakakin ya kara da cewa, an kuma samu kiran tashin gobara daga Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya da sauran cibiyoyi.

“Mun samu wani kira kan wata gobara a otal, inda muka tseratar da asarar dukiya ta kimanin Naira 400,000.

“Mun kuma samu kiraye-kiraye guda biyu kan gobarar shaguna tare da ceto dukiya da darajarsu ta kai Naira miliyan 14.9,” inji shi.

Bala ya danganta mafi yawan aukuwar gobarar da ake samu a jihar da rashin kula da amfani da gas din girki da kuma na’urorin wutar lantarki marasa inganci.

Ya shawarci mazauna jihar da su tabbatar sun tanadi abun kashe wutar gas da na’urorin wutar lantarki.

“A guji barin yara suna amfani da ashana ko wuta; a guji shan taba a kan gado,” inji shi.