✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: Gwamnati za ta tallafa wa ’yan kasuwar Nguru

Wannan gobara iftila'i ce daga Allah kuma sun karbe ta a matsayin kaddara.

Gwamnatin Jihar Yobe ta sha alwashin tallafa wa wadanda suka tafka asarar miliyoyin naira sakamakon gobarar da ta auku a Babbar kasuwar Nguru.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na Jihar Yobe (YOSEMA) Dokta Muhammad Mai Goje, ne ya bayyana wa wakilinmu hakan a lokacin da tawagar hukumar ta ziyarci kasuwar domin kididdige asarar da aka yi.

Dokta Goje, ya ce gwamna Mai Mala Buni ne ya umurce su da su fara aikin cikin gaggawa don ganin yadda za a taimaka wa ’yan kasuwar akan lokaci.

A cewarsa, tuni sun fara daukar bayanai da kuma musabbabin faruwar gobarar don dakile aukuwar makamanciyarta a nan gaba.

A nasa jawabin na jaje ga ’yan kasuwar, Shugaban Karamar Hukumar Nguru, Alhaji Modu Kachallah, cewa ya yi wannan gobara iftila’i ce daga Allah kuma sun karbe ta a matsayin kaddara.

Yadda aka rika fafutikar kwasar kayayyakinsu a lokacin da gobarar ta auku a Babbar kasuwar Nguru

Alhaji Modu, ya jinjina wa hukumar kashe gobara ta Nguru da al’ummar gari bisa daukin gaggawa da suka kawo wajen kashe wutar ta tsaya a iya dukiya ba tare da an rasa rai ba.

Ya kuma ce gwamnati ta nuna damuwarta matuka kan irin asarar da aka tafka sannan ta yi alkawarin za ta yi kokarin ganin ta bayar da tallafi cikin kankanin lokaci.

Kazalika, shi ma Shugaban Kungiyar ’yan kasuwar Nguru, Alhaji Ibrahim Yura, cewa ya yi wannan gobarar iftila’i ne da Allah, da Ya aiko don haka sun karbe ta da zuciya mai kyau bisa tabbacin cewa duk wanda Allah Ya jarrabe shi kuma ya ci  Zai mayar masa da mafificin alheri na asarar da ya yi.

Shi ma Sarkin Kasuwar, Alhaji Bala Kanta cewa yayi wannan gobara jarrabawa ce daga Allah yana rokon Allah Ya mayar musu da alheri.

Bala Kanta, ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnati da ta shiga lamarin ’yan kasuwar wajen ganin ta kai musu dauki cikin gaggawa saboda an tafka asara mai girma da har ta kai ga an samu wadanda ba su da halin samun abin da za su ci.

Kungiyar muryar talaka ta kasa reshen Jihar Yobe ta bakin mambanta, Kwamred Salisu Arnayau Nguru, ta jajanta wa ’yan kasuwar inda tace wannan asara ba ta tsaya kan ’yan kasuwar Nguru ko Yobe ba domin kuwa asara ce da ta shafi Najeriya baki daya.

Armayau ya sake yin kira ga gwamnatocin Yobe da na tarayya harma da daidaiku masu hannu da shuni da su kawo wa ’yan kasuwar Nguru dauki.

Aminiya ta ruwaito cewa, gobarar dai wadda ta auku a Babbar Kasurwa garin Nguru, ta faru ne a jiya asabar inda shaguna da dukiyoyi na miliyoyin naira suka salwanta da har yanzu ba a kayyade adadin asarar ba.

Wani ganau, Abubar Ibn Usman,  ya ce wutar ta shafe fiye da kimanin sa’o’i uku tana cin sashen ’yan gwanjo na kasuwar.

A cewarsa, shaguna da wuraren ajiye kayayyaki na miliyoyin Nairori sun kone a sakamakon gobarar.