✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta cinye kantuna 91 a kasuwar tufafi

Kantuna 91 suka kone kurmus a gobarar kasuwar tufafi ta Kairo a Jiha Legas.

Akalla kantuna 91 ne suka kone kurmus bayan gobara ta tashi a kasuwar tufafi ta Kairo a Jiha Legas.

Gobarar ta tashi ne a ranar Alhamis da dare, amma ba a kai ga kashe ta ba sai a safiyar Juma’a.

Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawat ta Jihar Legas (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce “Da muka isa wurin mun samu wasu kantuna da ke a kulle suna ci da wuta.”

Ya ce ba a yi asarar rai ba, amma an gano wasu abubuwan fashewa a yayin kashe gobarar kasuwar da ke unguwar Oshodi, kuma ana bincike a kai.

Ofisoshin gudanawar kasuwar da shaguna daban-daban ne gobarar ta lakume baya ga dukiyoyin miliyoyin Naira da aka yi asara.

LASEMA da hukumar kwana-kwana da sauransu ne suka yi taron dangi kafin a samu a kashe wutar.