✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta cinye rumfuna 252 a Kasuwar Abuja

An tafka a asara a gobarar da tawaga uku ta masu kashe wuta suka yi fama da ita

Akalla shaguna 252 na wucin gadi ne suka kone a gobarar da ta tashi a Kasuwar Galadima da ke unguwar Gwarimpa a Abuja.

Da misalin 1.30 na rana ne gobarar ta tashi lokacin Musulmai sun tafi Sallar Juma’a takwarorinsu Kiristoci kuma suna  hutun Kirsimeti.

“Gobarar ta tashi ne bayan an dawo da wutar lanatarki, ganin yanayin karfin da ta zo da shi, na umarci ma’itana suk kashe talabijin, kan ka ce kwabo wata waya ta fara tartsatsin wuta shaguna suka fara ce,” inji Falmata Bukar, wata daga cikin ’yan kasuwar.

Fatima ta ce gaba daya jarinta a shagonta na sayar da abinci da kayan tireda a kasuwar ya kone kurmus a gobara.

Regina Musa, mai shagon gyaran gashi ta ce, “Na aikatu sosai da dare a jaribirin gobarar saboda na yi ta fama da kwastomomi.

“Na tsara zuwa shago washegari amma sai na kasa fita saboda gajiyar da na yi.

“Wani makwabcina tela ne ya kira ya shaida min abin da ke faruwa. Duk abin da nake da shi sun kone: kama daga injina, janareto da tsabar kudi,” inji ta.

Wani tela ya shaida mana cewa kekunan dinkinsa da kayan mutanen da suka kawo musu dinkin duk sun kone a gobarar.

“Yawancinmu teloli mun yi asarar komai, ga kuma kayan mutanen da suka kawo dinkuna shagunanmu. Ba mu san yadda za mu biya su ba,” kamar yadda ya ce.

Shugaban kasuwar, Sulaiman Musa, ya ce gobarar ta lakume kaya na miliyoyin Naira.

Suleiman ya yaba wa ’yan kwana-kwana da suka kawo dauki a kan kari.

Ya ce tawaga uku na masu kashe gobara ne suka bayar da dauki da suka hada da na Birnin Tarayya, Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) da Rundunar Sojin Sama, duk sun isa wurin domin hana gobarar kama sauran gine-ginen da ke makwabtaka da kasuwar.