✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta hallaka dalibai 20 a Yamai

Dalibai 20 ake fargabar sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi cikin wata makarantar a Yamai, babban birnin Nijar. Kawo yanzu ba a iya…

Dalibai 20 ake fargabar sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi cikin wata makarantar a Yamai, babban birnin Nijar.

Kawo yanzu ba a iya gano musabbabin gobarar ba wacce ta tashi a cikin wani ajin daukan darussa na makarantar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa, gobarar ta soma ne a harabar shiga makarantar mai dauke da dalibai 800 a Kudu maso Gabashin Yamai daura da filin tashi da saukar jiragen sama.

Hakan ya sanya gobarar wacce ta yadu zuwa azuzuwa 20 da aka yi da kirage da zana, ta datse dalibai har suka galabaita sakamakon rashin samun hanyar tserewa.

Azuzuwa 20 ne gobarar ta lakume kuma an yi rashin sa’a yara 20 sun riga mu gidan gaskiya, a cewar Kanal Sidi Mohamed, Shugaban Hukumar Kwana-Kwana ta Kasar.

A cewar Halidou Mounkaila, Sakatare-Janar na Kungiyar Kwadago da Ma’aikatan Cibiyar Kananun Makarantu, ya ce “azuzuwa 25 daga cikin 38 ne gobarar ta kone, kuma an samu mutuwar yara 20.”

Wani malamin makarantar ya shaida cewa, “Babu hanyar fita idan bukatar gaggawa ta taso, inda dalibai da dama suka makale wasu kuma amma wasu sun yi kokarin tsallaka katanga.

“Galibin wadanda suka mutu yara ne daga kananan azuzuwa,” in ji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, a wata ziyarar jaje da Firaiminista Ouhoumoudou Mahamadou ya kai makarantar domin gane wa idanunsa ta’adin da gobarar ta yi, ya kuma yi ta’aziyya kan wadanda ibtila’in ya rutsa da su.