✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta hallaka masu COVID-19 18 a cibiyar killacesu a Indiya

Gobarar na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar a kullum a fadin duniya.

Wata gobara da ta tashi a wata cibiyar killace masu dauke da cutar COVID-19  a yammacin Indiya ta hallaka masu cutar 18.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar a kullum a fadin duniya.

Gobarar dai ta fara ne a hawa na farko na ginin asibitin Patel Welfare dake birnin Bhauruch, kuma jami’an kwana-kwana sun sami nasarar kasheta cikin sa’a daya, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi sun ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabinta.

Asibitin dai wanda aka kebe domin killace masu cutar na birnin Bhauruch, wanda ke da nisan kilomita 185 Arewa da babban birnin kasuwancin jihar na Ahmedabad.

Mataimakain Sufuritandan ’Yan Sanda na birnin Bhauruch, R.V. Chudasama ya ce, “Majinyatan cutar 16 da kuma ma’aikatan asibiti biyu sun rasu sakamakon wutar. 12 daga ciki kuma wuta da hayakin da suka turnuke ne suka kashesu.

“Binciken farko-farko ya nuna mana cewa tangardar wutar lantarki ce ta yi sanadiyyar tashin gobarar,” inji shi.

To sai dai wani jami’in gwamnati, Dushyant Patel ya ta’allaka gobarar da hujewar wata tukunyar adana iskar Oxygen da masu cutar ke shaka, wacce kuma ake adanawa a sashen tallafawa wadanda cutar ta yi musu tsanani.

Kafafen watsa labaran yankin sun nuna hotunan yadda sashen asibitin da lamarin ya shafa ya kone kurmus.

Tuni Fira Ministan kasar, Narendra Modi ya nuna alhini da kaduwarsa sakamakon tashin gobarar.

Ko a ranar Asabar din da ta gabata sai da Indiya ta kafa tarihin samun sabbin kamuwa da cutar kimanin 401,993 a kwana daya, lamarin da ya kawo yawan alkaluman masu dauke da ita zuwa miliyan 19.1.

Bugu da kari, wasu karin mutum 3,523 sun mutu a rana daya, yayin da jimlar wadanda suka mutu ya haura 211,853, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta kasar ta tabbatar.

Sai dai masana na ganin cewa alkaluman na iya zarce hakan nesa ba kusa ba.