✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kama a gidan Man Conoil a birnin Lafia

Wutar ta kama ne lokacin da motar dakon mai take sauke man fetur din da ta dauko.

Gidan Sayar da Man Fetur na Conoil da ke birnin Lafia a jihar Nasarawa ya kama da wuta.

Wasu wanda lamarin ya faru akan idonsu, sun bayyana cewa wutar ta kama ne a daren ranar Juma’a, inda ta kama wasu shaguna dake jikin gidan man kafin daga bisani a kashe wutar.

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Nasarawa, Alhaji Dalhatu Dogara ya tabbatar da afkuwar lamarin

Ya bayyana cewa wutar ta kama ne lokacin da motar ta sauke man zuwa manyan tankuna dake kasa.

Sai dai ya yi kira da masu gidajen mai da su rika lura da matakan kariya a yayin da ake sauke musu mai.

A cewarsa ya kamata ake ba da wasu awanni kafin sauke mai idan motar dakon man ta kawo.

Sannan ya bayyana cewa jami’ansu sun yi nasarar kashe wutar cikin sa’a daya.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wakilin gidan man, amma bai ce komai ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.